Majalisa ta amince ma Buhari ya sake antayo ma Najeriya bashin N850,000,000,000

Majalisa ta amince ma Buhari ya sake antayo ma Najeriya bashin N850,000,000,000

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dattawa ta amince masa ya ciyo bashin naira biliyan 850 don gudanar da manyan ayyuka dake cikin kasafin kudin shekarar 2020.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito Buhari ya bayyana bukatar hakan ne cikin wata wasika daya aika ma shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan.

KU KARANTA: Wata Iska mai karfin gaske ta kashe mutane 2 a Taraba, ta lalata gidaje 500

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karanta wasikar shugaban kasar ne a zauren majalisar a yayin zamanta na ranar Talata, 28 ga watan Afrilu.

A cewar shugaban kasar, gwamnati na bukatar ciyo bashin ne a cikin gida domin tabbatar da ta gudanar tare da kammala wasu manyan ayyuka dake cikin kasafin kudin 2020.

Majalisa ta amince ma Buhari ya sake antayo ma Najeriya bashin N850,000,000,000
Majalisa ta amince ma Buhari ya sake antayo ma Najeriya bashin N850,000,000,000
Asali: UGC

Bayan karanta wasikar, majalisar ta amince da bukatar shugaban kasa na ciyo bashin, sa’annan ta umarci kwamitin kudi ta nemo karin bayani daga ministar kudi game da bashin.

Wannan shi ne zama na farko da majalisar ta yi tun bayan tafiya hutun coronavirus da ta yi tsawon makonni 5 da suka gabata.

Sai dai shugaban majalisar ya bayyana dalilinsu na dawowa bakin aiki shi ne domin taimakawa wajen yaki da annobar Coronavirus tare da daidaita al’amurar kiwon lafiya a kasar.

Ya kara da cewa cutar ta shafi kasafin kudin 2020, don haka hakkin majalisa ne ta yi aiki tare da bangaren zartarwa domin shawo kan duk matsalolin da ka iya tasowa.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kano ta bayyana cewa ta gano dalilan da suka kawo mace macen da aka dinga samu a jahar a makon da ta gabata.

A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.

Gwamnatin tace sun gano haka ne bayan gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel