Aron kudi: ‘Yan Majalisa sun binciko maganar damka arzikin Najeriya hannun Sinawa

Aron kudi: ‘Yan Majalisa sun binciko maganar damka arzikin Najeriya hannun Sinawa

- Majalisa ta gano wani sharadi a cikin yarjejeniyar bashin Najeriya da Sin

- A 2018 gwamnatin tarayya ta nemi aron kudi daga wani bankin kasar Sin

- Daga cikin sharadin bashin shi ne bada iko da Najeriya idan aka gaza biya

A ranar Talata, 28 ga watan Yuli, 2020, majalisar wakilan tarayya, ta ce ta gano wasu sharuda masu hadari da aka cusa a yarjejeniyar bashin da Najeriya za ta karbo daga Sin.

A sashe na 8(1) na takardar yarjejeniyar karbar aron kudi tsakanin gwamnatin Najeriya da bankin ‘Export-Import Bank of China’ na Sin, an ba kasar Asiyar iko da dukiyar Najeriya.

Majalisar wakilai ta na zargin cewa a wannan bashi na Dala miliyan 400 da aka karbo a 2018, gwamnati ta bada ikon damkawa Sin wanda ta ba ta aron kudi, iko da kasar ta.

Idan abin da jaridar This Day ta rahoto ta tabbata, muddin gwamnatin tarayya ta gaza biyan wannan bashi, dukiyar Najeriya za ta iya komawa hannun kasar, ko ta ki, ko ta so.

KU KARANTA: Ministan kasar Zimbabwe da aka hada baki da shi aka kifar da Mugabe ya mutu

Aron kudi: ‘Yan Majalisa sun binciko maganar damka Najeriya hannun Sinawa
Majalisar wakilai Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Abin da sashen yarjejeniyar ya ce shi ne: “Mai neman bashi ya janye duk wani iko na kasa ko zaman-kai ko iko da dukiyarsa idan har ya sabawa sharadin da aka yanke a sashe na 8(5), don haka za a karbe iko da duk wani arzikinsa, face kadarorin sojoji da na kasashen da ake zaman lafiya da su.”

Togaciyar da sharadin ya yi shi ne a kan kadarorin sojojin kasar da kuma na kasashen da ke zaman aminci da Najeriya.

Ma’aikatar kudi ce ta sa hannu a madadin gwamnatin kasar wajen karbo wannan bashi. A kudi Najeriya, abin da kasar ta karbi aro daga Sin ya haura Naira biliyan 150.

A dalilin haka ne majalisar ta yanke hukuncin kiran ministocin kasar; Rotimi Amaechi; Isa Pantami; da Zainab Ahmed domin su yi karin bayani game da sharadin bashin da ake karba.

Ministan sufuri ya nemi majalisa ta dakatar da wannan bincike da ta ke yi har sai an karbo aron kudin aikin dogo daga kasar Sin domin binciken ya na iya hana kasar ta bada kudin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel