Gwamnatin Buhari ta karbowa Najeriya aron kudi N18.89tr daga 2015

Gwamnatin Buhari ta karbowa Najeriya aron kudi N18.89tr daga 2015

- Ana bin Najeriya bashin Naira Tiriliyan 30 ko Dala Biliyan 85 a yanzu

- Gwamnatin Shugaba Buhari ce ta karbo aron kusan Naira Tiriliyan 20

- A shekaru biyar na mulkin APC, bashin kasar ya karu da fiye da 150%

Bashin da ke kan wuyan Najeriya ya haura Naira tiriliyan 30 a karshen watan Yunin bana, inji hukumar da ke kula da bashi na kasa watau DMO.

A ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, 2020, hukumar DMO ta bada sanarwar cewa kudin da ake bin gwamnatin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 31.01.

Abin da wannan ya ke nufi shi ne daga lokacin da Muhammadu Buhari ya karbi mulki zuwa yanzu, bashin da Najeriya ta ci ya karu sosai da gaske.

KU KARANTA: Buhari ya fadawa Ministoci yadda za su nemi iznin ganinsa

Rahoton da jaridar Punch ta fitar ya nuna cewa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbo aron Naira tiriliyan 18.89 a cikin shekaru biyar.

Gwamnatocin jihohi 36 su na da kaso a cikin bashin da aka karbo a kasar, DMO ta ce kason gwamnatin tarayya ya fi yawa domin ita ce kan gaba wajen cin bashi.

Daga cikin bashin Naira tiriliyan 30 da ake bin Najeriya, kason gwamnatin tarayya ya kai kusan tiriliyan 25, kimanin 80% na adadin bashin da ke kan wuyan kasar.

Tsakanin 2015 zuwa tsakiyar shekarar nan Najeriya ta karbo aron wadannan makudan kudi.

KU KARANTA: Buhari ya bada umarnin fitar da kudin da za su zaburar da tattalin kasa

Gwamnatin Buhari ta karbowa Najeriya aron kudi N18.89tr daga 2015
Ministar kudin Najeriya, Zainab Ahmed Hoto: Nairametrics
Asali: Twitter

DMO ta ce a cikin watanni uku kawai sai da alkaluman bashin kasar su ka karu da Naira tiriliyan 2.38. Ma’ana gwamnati na cin bashin fiye da Naira biliyan 500 duk wata.

A kudin Dalar Amurka, bashin da ake bin gwamnatin Najeriya shi ne Dala fam biliyan 85.97.

An samu karuwar wannan adadi ne a sakamakon sabon bashin da kasar ta karbo daga hukumar bada lamuni ta Duniya watau IMF domin aiwatar da ayyukan kasafin 2020.

Bugu da kari, Najeriya ta na shirin karbo wasu bashin daga bankin cigaban Afrika, babban bankin Duniya da kuma bankin musulunci, duk a cikin wannan shekara da ake ciki.

Ana kukan cewa gwamnatin APC ta cika yawan cin bashi, ita kuma ta kan kare kanta da cewa har yanzu bashin da ke kan wuyan kasar bai kai a tada hankali a kansa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel