Mabiya Abduljabbar Kabara sun fara fitowa, su na tuba bayan Shehi ya yi karo da Malaman Kano

Mabiya Abduljabbar Kabara sun fara fitowa, su na tuba bayan Shehi ya yi karo da Malaman Kano

  • Almajiran Abduljabbar Nasiru Kabara suna dawowa daga rakiyarsa a Kano
  • Yanzu wasu sun fito shafukansu na Facebook, su na neman afuwar al’umma
  • Sani Oris ya ce zai kona masallacin Abduljabbar idan har aka sake bude shi

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wasu almajiran da suke tare da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, sun fara barranta kansu daga tafiyar da suke kai a da.

Daliban na sa sun tabbatar da janye mubaya’ar da su ka yi wa shehin malamin, har wasu suna cewa sun yi da na-sanin abin da su ka yi, suna neman gafara.

Wani daga cikin su shi ne Auwal Alqaseem Mairiga wanda ya ce ya fi kowa kaunar malamin kafin a zauna, Auwal Mairiga ce ya dawo daga rakiyarsa yanzu.

KU KARANTA: Za a gurfanar da Abduljabbar Kabara a gaban Alkali

“Mun ga yadda ta wakana da Alqasim Hotoro. Mun ga yadda ta wakana a wayar da su ka yi da Umar Rijiyar Lemu. Mun ji yadda ta wakana a muqabalar da aka yi jiya.”

Kara karanta wannan

Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahara Buhari

Auwal Alqaseem Mairiga ya ce da ya kunyata idan ya je lahira, ya zabi ya ji kunya a gidan Duniya.

Haka zalika wani Abdulrasheed Adamu Sani wanda yake tare da shehin kafin zamansa da sauran malaman Kano, ya ce ya fahimci ba su bane a kan gaskiya.

“Saboda haka ni na karbi wannan gaskiyar. Allah ya kara nuna mana gaskiya, ya ba mu ikon bin ta a duk inda ta ke. Ameen.”

Har ila yau akwai wani mai suna Alhaji Muhammad Aljabbary wanda shi ma mabiyin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda yanzu ya janye kafa.

KU KARANTA: Tambayoyin da aka jefawa Sheikh Abduljabbar Kabara a Muqabala

Mabiya Abduljabbar Kabara sun fara fitowa, su na tuba bayan Shehi ya yi karo da Malaman Kano
Abduljabbar Kabara Hoto: www.dw.com/ha
Asali: UGC

A shafinsa na Facebook, Aljabbary ya bayyana matsayarsa a kan muqabalar da aka yi, ya ce ya so ace shehinsu ne ya yi nasara, amma sai akasin hakan ta faru.

“Jiya na kalli cikakken bidiyon, amma malam ya gaza amsa mafi yawan tambayoyin da aka yi masa, don haka ni Muhammad Abdallah Aljabbary ba na tare da jagora a nan domin sun fi mu gaskiya.”

Kara karanta wannan

Bayan shekaru biyu da zabe, Buhari ya bayyana abin da ya sa APC ta rasa wasu jihohi a 2019

“Ina ba wa wadanda ba su ji dadin kalamai na ba hakuri, domin ni ma ba haka na so ba.”

Shi ma wani matashi mai suna Sani Oris da ya bar tafiyar Kogo ya na cewa zai kona masallacin Abduljabbar Kabara muddin gwamnati ta yarda ta sake bude shi.

Kun ji cewa Kwamishinan addinai na Kano, Dr. Muhammad Tahar Adam, bai yarda da tubar da Sheikh Abduljabbar Kabara ya yi bayan an kamma muqabala ba

Baba Impossible ya ce a addinin Musulunci, babu tuba ga wanda ya taba Annabi SAW, sannan ya ja kunnen masu neman tada rigima da su guji saba wa dokar kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel