Wata mata ta shiga wajen bikin cikarta shekaru 50 a akwatin gawa, bidiyon ya haddasa cece-kuce

Wata mata ta shiga wajen bikin cikarta shekaru 50 a akwatin gawa, bidiyon ya haddasa cece-kuce

  • Wata baiwar Allah tayi bikin cikar ta shekaru 50 a cikin wani yanayi da ba a saba gani ba lamarin da ya jefa kafafen sada zumunta cikin rudani
  • A cikin bidiyon da ke yawo, matar ta isa wurin da za a yi bikin ranar haihuwar a cikin akwatin gawa na gilashi
  • Bayan ta isa cikin yanayi da ba a saba gani ba, an taimaka mata ta fito sannan aka mika mata lasifika inda ta rera waka

Zagayowar ranar haihuwa lokaci ne na musamman a rayuwar mutum kuma wata baiwar Allah ta yi nata cikin wani yanayi da ba za a taba mantawa da shi ba.

Matar wacce ta zama abun magana a shafukan sada zumunta tayi bikin cikar ta shekaru 50 a duniya sannan ta isa wurin taron cikin wani yanayi da ba a saba gani ba.

KU KARANTA KUMA: Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

Wata mata ta shiga wajen bikin cikarta shekaru 50 a akwatin gawa, bidiyon ya haddasa cece-kuce
An gano matar a cikin akwatin gilashi Hoto: @gossipboyz1
Asali: Instagram

A cikin bidiyon da @gossipboyz1 ya wallafa a Instagram, an kawo matar wurin taron a cikin akwatin gawa na gilashi.

Yayinda ta isa wurin, baƙi sun taimaka mata wajen fitowa daga cikin akwatin. Daga nan sai aka bai wa matar da ba a san ko wacece ba lasifika inda ta rera waka don burge bakin.

An yi cece-kuce kan bidiyon

@goglownatural_skincare ta rubuta:

"Me wannan ke nufi yanzu idan an fada mata cewa za ta mutu yanzu za ta fara kuka.”

@sharon_jamaican_biafan ya ce:

"Menene dalilinta na aikata hakan? Abin rashin tunani da na gani a yau!"

KU KARANTA KUMA: Bidiyo ya nuna lokacin da mai martaba sarkin Kajuru ya fashe da kuka bayan masu satar mutane sun sako shi

@scopicsgg yayi sharhi:

"Ba zan iya kallon zuwa karshen ba, da gaske abubuwa suna faruwa a wannan duniyar."

@pappy_horris ya bayyana:

"Da ta mutu a cikin akwatin ko dai wannan na yiwa Ubangiji ba’a ne.”

Kara karanta wannan

Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

A wani labarin, wani mai ikirarin Fasto ne shi mai suna Omosebi Fred, ya gurfana a gaban kotu kan zargin karkatar da kudin cocin har na naira miliyan 15 da rabi.

An gurfanar da Adeola a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja da Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) kan tuhume-tuhume 11 kan zargin karkatar da kudin cocin.

Zarge-zargen, a cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa, sun hada da zargin "hada baki da cin amanar mukamin ofis da karkatar da kudade."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng