'Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun ƙwayoyi

'Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun ƙwayoyi

  • Yan sanda sun cafke wani da ake zargin dillalin miyagun kwayoyi ne na IPOB
  • An kama wanda ake zargin ne Nnamuka Uchenna a gidansa da ke Njaba a Imo
  • An kama shi ne bayan kama wani direba da wata yarinya da ke masa aiki a jihar

Rundunar yan sandan jihar Imo ta ce ta kama Nnamuka Uchenna, wani da ake zargi dillalin miyagun ƙwayoyi ne da ke sayarwa mambonin kungiyar IPOB da ESN kwayoyi, rahoton The Cable.

SaharaReporters ta ruwaito cewa an kama Uchenna ne a gidansa da ke Umuaka a ƙaramar hukumar Njaba a ranar 8 ga watan Yuli inda aka gano wasu abubuwa da ake zargin hodar Iblis ne da kudinsu ya kai Naira miliyan 150.

'Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun ƙwayoyi
'Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun ƙwayoyi. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

An kama shi ne tare da wani Chinedu Ukaegbulam da Augustine Ete.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama dilan ESN/IPOB na miyagun kwayoyi, an samu kwayoyin N150m

A cewar The Nation, majiyoyi daga rundunar yan sanda an kama wadanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri da ya yi sanadin kama wani Obinna Ohaji wanda ya yi sojan gona matsayin direba yana neman fasinjoji a mota kirar Nissan Caravan.

An gano hodar iblis mai dimbin yawa a cikin motar bayan da aka bincika.

Bayan yan sanda sun masa tambayoyi, ya amsa cewa an aike shi ya kaiwa wata mata hodar Iblis ɗin ne a Elele jihar Rivers.

KU KARANTA: Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta

An ce ya kai yan sanda wurin wata yarinya mai shekaru 17 da ta amsa cewa ita ce ke samarwa kungiyar miyagun kwayoyin a jihar Rivers.

Micheal Abattam, kakakin yan sandan jihar ya ce akwai yiwuwar wadanda aka zargin su ke raba wa ƴan IPOB muggan kwayoyi a sansanin su a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari Baki Ɗaya Saboda Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

A cewarsa ana cigaba da bincike domin gano inda muggan kwayoyin suka fito a jihar sannan an kama wasu yan kungiyar.

An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

A wani labarin, Ƴan sanda a jihar Niger sun yi holen wasu mutane uku da ake zargi da mallakar kudaden jabu ƴan dubu-dubu da adadinsu ya kai Naira miliyan 15.8, Guardian NG ta ruwaito.

Wadanda ake zargin sune Fasto Sabastine Dabu, ɗan shekara 48 daga Zuru, jihar Kebbi, Emmanuel Aka Zuwa, ɗan shekara 42 daga ƙauyen Adi, ƙaramar hukumar Buruku, jihar Benue da Umar Mohammed, ɗan shekara 50 daga Pandagori, ƙaramar hukumar Rafi, jihar Niger.

Guardian ta ruwaito cewa yayin holen wadanda ake zargin a hedkwatar yan sanda a Minna, kakakin yan sanda Wasiu Abiodun ya yi bayanin cewa ƴan sandan ƙaramar hukumar Kontagora, jihar Niger ne suka kama su.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel