Da Ɗumi-Ɗumi: Jerin Sunayen Sakatarorin Dindindin 5 da Buhari Ya Rantsar

Da Ɗumi-Ɗumi: Jerin Sunayen Sakatarorin Dindindin 5 da Buhari Ya Rantsar

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin biyar
  • An rantsar da sakatarorin ne a ranar Laraba a fadar shugaba kasa kafin taron FEC
  • Sakatarorin da aka nada sun fito ne daga jihohin Nasarawa, Ekiti, Enugu, Legas da Katsina

Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin a ma'aikatun gwamnati da ke fadin tarayya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Leadership ta ruwaito cewa an rantsar da su ne kafin fara zaman majalisar zartarwa ta tarayya, FEC, da aka yi a ranar Laraba.

KU KARANTA: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Sakatarorin Dindindin 5
Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Sakatarorin Dindindin 5. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Mu Dakatar Da Rochas Okorocha Ba, Inji Jam’iyyar APC

Sakatarorin dindindin din da aka nada sun hada da:

  1. Ibrahim Yusuf daga jihar Katsina,
  2. Olusesan Adebiyi (Jihar Ekiti),
  3. Maryanne Onwudiwe (Jihar Enugu),
  4. Marcus Ogunbiyi (Jihar Lagos) da
  5. Ibrahim Abubakar Kana (jihar Nasarawa).

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Wadanda suka hallarci taron na FEC sun hada da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Ibrahim Gambari.

Ministocin da suka hallarci taron na FEC

Saura sun hada da ministoci takwas har da ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, Ministan Shari'a kuma Attoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire.

Sannan Ministan Harkokin Yan sanda, Muhammad Dingyaɗi da na makamashi, Mamman Saleh, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu da na Sufuri, Rotimi Ameachi.

Shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Folashade Yemi-Esan da sauran ministocin sun hallarci taron daga ofisoshinsu ta a Abuja ta hanyar fasahar intanet mai bidiyo da murya.

Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta

A wani labari daban, Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya ce Nigeria ta yi matukar sa'a duba da cewa kallubale masu wahala da ta ci karo da su basu raba kasar ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bikin babban Sallah: Masarautar Daura ta bayyana matsayarta a kan Hawan Sallah

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kasar ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati a Abuja, yayin da ya ke karbar rahoton taron tsaro na kasa da Majalisar Wakilai na tarayya ta yi a ranar 26 ga watan Mayun 2021.

Tawagar mambobin yan majalisar wakilai na tarayya karkashin jagorancin kakakin majalisa Femi Gbajabiamila ne ta kai wa Buhari rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel