Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Mu Dakatar Da Rochas Okorocha Ba, Inji Jam’iyyar APC

Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Mu Dakatar Da Rochas Okorocha Ba, Inji Jam’iyyar APC

  • Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta karyata cewa ta dakatar da Rochas Okorocha
  • Jam'iyyar mai mulki ta ce wasu masu nufin kitsa sharri ne suka wallafa wasikar bogi na dakatarwar
  • APC ta bukaci jama'a suyi watsi da labarin bogin sannan ta bukaci kafafen watsa labarai su rika tuntubar sanannun kafafen watsa labarai na jam'iyyar

Kwamitin rikon kwarya da tsara gangami, CECPC, na All Progressives Congress (APC) ta musanta dakatar da Senator Rochas Okorocha, Daily Trust ta ruwaito.

Da farko, an rika baza wani wasika a dandalin sada zumunta da ke cewa an dakatar da Okorocha.

Amma cikin wata sanarwar da sakataren CECPC, John James Akpanudoedehe ya fitar a daren ranar Talata, ya ce wasikar ta jabu ne da aka kirkira.

DUBA WANNAN: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Mu Dakatar Da Rochas Okorocha Ba, Inji Jam’iyyar APC
Ba Mu Dakatar Da Rochas Okorocha Ba, Inji Jam’iyyar APC. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Don haka ya bukaci jama'a su yi watsi da abin da wasikar ta kunsa da ya ce wasu masu son tada zaune tsaye ne suka kirkira.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Uwar jam'iyya ta dakatad da Rochas Okorocha daga APC

Sanarwar ta ce:

"Masu yadda labaran jabu sunyi amfani da damar ganin wasikar da muka aike wa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, suka kwafa saka hannun shugaban CECPC da sakatarensa daga wasikar bogi.
"APC bata da kwamitin ayyuka a yanzu kamar yadda wasikar ta ce sai dai kwamitin riko da tsara gangami na musamman, CECPC wadda aka daura wa alhakin sauya alkalar jam'iyyar da hada kai da karfafa jam'iyyar mu.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Imo Ta Rufe Makarantar Rochas Okorocha a Owerri

"Muna kira ga al'umma suyi takastantsan da masu yada labaran karya da masu nufin kitsa sharri da ke amfani da kowane dama domin tada rikici ta hanyar watsa labaran bogi. Muna kuma kira ga yan jarida su rika dogaro da sanannun kafafenmu na watsa labarai domin samun bayanni kan ayyukan jam'iyyar.
"Muna kira ga al'umma su yi watsi da wasikar domin babu gaskiya a cikinsa."

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

An sanar da ranar fara taron gangamin jam'iyyar APC

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa ta tsayar da ranar 31 ga watan Yulin 2021 domin fara gangamin tarurukanta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da farko, jam'iyyar ta dage yin tarurukan har sai masha Allah wanda hakan ya haifar da cece-kuce.

Amma cikin wata wasika mai kwanan wata na 11 ga watan Yuli, Gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC da Sanata John James Akpanudoedehe, sakataren jam'iyyar sun sanar da sabon ranar fara tarurukan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel