Gwamnan jihar Osun ya wajabtawa kowane Ma’aikaci da Jami'i sa kaya iri-daya zuwa ofis

Gwamnan jihar Osun ya wajabtawa kowane Ma’aikaci da Jami'i sa kaya iri-daya zuwa ofis

  • Gwamnatin Adegboyega Oyetola ta kirkiro amfani da Adire Osun duk mako
  • A kowace ranar Alhamis, ma’aikatan gwamnati za su rika sa wannan tufafin
  • Gwamnan Osun ya yi wannan ne domin a farfado da al’adu da kawo aikin yi

Mai girma gwamnan jihar Osun, Mista Adegboyega Oyetola, ya wajabta wa duka ma’aikata da jami’an gwamnatin jiha amfani da tufafi iri daya.

Jaridar Tribune ta fitar da rahoto cewa Adegboyega Oyetola ya bukaci ma’aikata su rika sanya rigar Adire Osun a kowace ranar Alhamis ta Duniya.

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne domin ya tallata tufafin Adire Osun da ake yi a jiharsa.

KU KARANTA: Akwai bukatar a ragewa Gwamnatin Tarayya iko – Gwamnonin Yarbawa

Punch ta ce bayan wajabta amfani da wadannan tufafi, Adegboyega Oyetola ya tsaida kowace ranar Alhamis ta mako a matsayin ranar Adire Osun.

Gwamna Adegboyega Oyetola ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fito daga bakin sakataren yada labarai na jihar, Mista Ismail Omipidan.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Omipidan ya fitar da jawabin da ya yi wa take: ‘Osun Int’l Feashion Week: Oyetola launches mass production of Adire Osun …declares every Thursday Adire Osun Day’.

Gwamnan ya ce wannan samfuri na tufafi ya yi fice a Osun, ya ce ba a banza ake kiran garin Osogbo da Ilu Aro saboda irin sunan da su kayi a rinin kaya.

KU KARANTA: Rotimi Amaechi ya ce an karbe kwangilar titin jirgin Maiduguri

Gwamnan Osun
Gboyega Oyetola na jihar Osun Hoto: /www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Omipidan ya ke cewa gwamnatin Adegboyega Oyetola ta kawo wannan ne domin a farfado da tunanin mutanen jihar Osun wajen ganin girman al’adarsu.

Sakataren gwamnatin Osun, Mista Prince Wole Oyebamiji shi ne ya wakilci Adegboyega Oyetola a wajen wannan taro da aka yi, ya na alwashin habaka jihar.

Prince Wole Oyebamiji ya ce gwamnatin Adegboyega Oyetola za ta yi kokari wajen nemo wa matasa aikin yi domin a bunkasa kudin shiga da ake samu.

Kwanaki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi dalilin jajircewa a kan yin zaben gaskiya da gaskiya a 2019, wanda hakan ya sa PDP ta karbe wasu jihohi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun gano rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga

Shugaba Buhari ya ce ya yi murna da Gwamna Ben Ayade da Bello Matawalle su ka shigo APC yanzu. Buhari ya yi wannan jawabi ne da su ka gana a Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng