Bello Matawalle: APC ta dauki matakin da zai harzuka Jiga-jigan Jam'iyya a Zamfara
- Kwamitin rikon kwarya ya kori shugabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara
- Sanata John Akpanuodedehe ya bada sanarwar nan a wata takarda da ya fitar
- An nada kwamitin mutane uku da za su ja ragamar jam’iyyar APC kafin zabe
Kwamitin shirya babban gangami da zabe, da rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa watau CECPC ya sauke shugabannin APC da ke jihar Zamfara.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, 2021, cewa CECPC ta sanar da shugabannin rikon kwarya na Zamfara cewa an sauke su.
John Akpanuodedehe ya aika wa Lawal Liman wasika
Sakataren rikon kwarya na kasa, Sanata John Akpanuodedehe, ya rubuta wa Lawal Liman takarda a ranar 9 ga watan Yuli, ya sanar da wannan mataki.
KU KARANTA: Matawalle ne Jagoran kowa a APC a Zamfara - Yariman Bakura
Hukumar dillacin labarai na kasa ta samu wannan takarda wanda ta isa Gusau a ranar Asabar, ta sallami shugabannin jam’iyyar ba tare da bata lokaci ba.
“Na rubuta wannan domin sanar da kai cewa bayan abubuwan da suka wakana a jam’iyya, kwamitin shirya babban gangami da zabe, da rikon kwarya ya amince da ruguza duka shugabannin jiha (mazabu, kananan hukumomi da shugabannin jiha)."
“Za a dauki wannan mataki ne da gaggawa.”
An kafa kwamitin mutane uku da za su shagoranci jam’iyyar APC a Zamfara. Kwamitin ya na karkashin Sanatan Zamfara ta tsakiya, Hassan Mohammed.
KU KARANTA: Agabi zai kalubalanci ‘Yan siyasa 33 da su ka sauya-sheka a Zamfara
Tsohon mataimakin gwamna, Muntari Anka shi ne mataimakin shugaban kwamitin yayin da tsohon SSG, Farfesa Abdullahi Shinkafi shi ne sakatarensu.
NAN ta ce kwamitin CECPC ya gode wa wadanda aka sauke saboda irin kokarin da su kayi a baya, tare da kira su ba sababbin shugabannin rikon goyon-baya.
Inda za a samu matsala da manyan jam'iyya
Wannan matakin da aka dauka ba dole ba ne ya yi wa wasu jiga-jigan jam’iyyar ta APC dadi, inda irinsu Sanata Kabiru Marafa suna ganin hakan ya saba wa doka.
Tsohon Sanatan na Zamfara ya soki jawo Bello Matawalle da aka yi zuwa APC tun da bai ci zabe ba, sannan ya yi tir da yunkurin korar shugabannin jihar da aka yi.
Asali: Legit.ng