Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Imo Ta Rufe Makarantar Rochas Okorocha a Owerri

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Imo Ta Rufe Makarantar Rochas Okorocha a Owerri

  • Gwamnatin jihar Imo ta rufe makarantar tsohon gwamnan jihar Rochas Okorocha da ke Owerri
  • Modestus Nwamkpa, hadimin gwamna Hope Uzodinma ya tabbatar da hakan yana mai cewa kayan jihar ne da Okorocha ya wuwushe
  • A bangarensa, hadimin Okorocha ya ce wannan kawai wani yunkuri ne na kawar da hankalin mutanen Imo daga talauci da yunwa da ke adabarsu

Gwamnatin Jihar Imo, a ranar Talata ta rufe makarantar tsohon gwamna Rochas Okorocha mai suna Rochas Foundation College da ke Orji, a Owerri babban birnin jihar, The Punch ta ruwaito.

Jami'an gwamnati sun isa wurin da makarantar ya ke, wacce tsohon gidajen ma'aikatan gidan rediyon jihar Imo ne sannan suka rufe wurin.

Wakilin The Punch, wanda ya ziyarci wurin ya ga babban ginin da a yanzu gwamnatin jihar ta amshe.

DUBA WANNAN: Sojoji Sun Ceto Mutum 17 Bayan Ragargazan Ƴan Boko Haram a Borno

Kara karanta wannan

COVID-19: Yadda Najeriya ta kunyata masana - Aregbesola

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Imo Ta Rufe Makarantar Rochas Okorocha a Owerri
Tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha da Gwamnan Imo Hopr Uzodinma. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Babban mashawarcin gwamnan na musamman kan jaridu, Modestus Nwamkpa, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce, gwamnan jihar, Hope Uzodinma, ba zai yi kasa a gwiwa ba wurin amsa kayayyakin jihar da ake zargin 'Okorocha da iyalansa sun sace'.

Nwamkpa ya ce gwamnan ba wani sabon abu ya ke yi ba illa aiwatar da shawarwarin da kwamitocin bincike daban-daban da aka kafa suka bayar.

Martanin Gwamna Okorocha game da rufe makarantar

Mai magana da yawun gwamna Rochas Okorocha, Sam Onwuemeodo, da aka tuntube shi ya ce nasarorin da Okorocha ya samu da abin da ya cimma a matsayinsa na dan siyasa na tsolewa Uzodinma ido.

KU KARANTA: 2023: Ku Dena Cewa Tilas Ne a Baku Mulki, Zulum Ya Gargaɗi Gwamnonin Kudu

Hadimin na Okorocha ya ce:

"Wannan shine karo na hudu da gwamnatin jihar Imo ke sanar da cewa ta rufe wannan wurin. EFCC ita ma ta sanar cewa ta rufe wurin amma gaskiya shine Uzodinma ya farka daga barcinsa. Akwai yunwa a jihar."

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari Baki Ɗaya Saboda Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

"Wannan kawai wata yunkuri ne fara sabon yaki da Okorocha da sauran jiga-jigan APC a jihar Imo da sakatariyar APC na kasa. Duk lokacin da Uzodinma ya lura mutane ba su jin dadin salon mulkinsa, sai ya yi amfani da sunan Okorocha don kawar da hankalin mutane amma gaskiya shine yunwa da talauci na adabar mutane. Ya ajiye girman kai ya tuntubi Okorocha ya koya masa yadda zai mulki jihar."

Zamfara: Ba za mu bari abin da ya faru da APC a 2019 ya sake faruwa ba, Yeriman Bakura

A wani labarin daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma mai neman takarar shugabancin kasa a ƙarƙashin Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Sani Yerima, ya ce masu ruwa da tsaki a siyasar jihar za su haɗa kai don ganin ba a maimaita abin da ya faru a 2019 ba, rahoton Daily Trust.

Kotun koli ta soke kuri'un APC a zaben 2019 a jihar Zamfara don jam'iyyar bata da ikon tsayar da ƴan takara don bata yi zaben fidda gwani ba yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

A hirar da ya yi da manema labarai a karshen mako a Abuja, Yerima ya ce babu rikici a jam'iyyar APC ta Zamfara kan shigowar Gwamna Bello Matawalle cikin jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164