2023: Ku Dena Cewa Tilas Ne a Baku Mulki, Zulum Ya Gargaɗi Gwamnonin Kudu
- Farfesa Babagana Zulum ya gargadi masu cewa tilas ne mulkin ƙasa ya koma kudu a 2023
- Gwamnan na jihar Borno ya ce yana goyon bayan a bawa kudu mulki bisa kan alƙawarin karba-karba amma a dena cewa dole
- Zulum ya ce ya kamata ƴan siyasa su zauna tare a teburi guda su tattauna batun ta yadda za a waranye lafiya
Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ce ba dole bane kudancin Nigeria ta fitar da shugaban ƙasa na gaba, The Cable ta ruwaito.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne a matsayin martani kan matsayar da takwarorinsa na kudu suka yi.
DUBA WANNAN: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno
A ranar Litinin, gwamnonin jihohin kudu 17 bayan taron da suka yi a gidan gwamnatin Legas sun ce 'kudu ne za ta fitar da shugaban ƙasa na gaba' bisa tsarin siyasar adalci da daidaito.
Da ya ke martani kan cigaban, Zulum, yayin hira da aka yi da shi a Channels TV, ya jadada goyon bayansa ga Kudancin kasar na fitar da shugaban ƙasa amma ya gargadi amfani da kalmar 'dole' yayin tattaunawa batun.
KU KARANTA: Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara
Ya ce akwai bukatar yin tattaunawa sosai dangane da lamarin.
Ya ce:
"Na sha nanatawa ba adadi, Ni Farfesa Babagana Zulum, ina ra'ayin shugabancin kasa ya koma kudu a 2023 saboda hadin kan kasar mu na da muhimmanci."
"Na biyu, tafiya tare da kowa yana da amfani. Na uku, na kasance a jam'iyyar APC, shekaru shida ko bakwai da suka gabata an bawa arewa damar fitar da ɗan takara kan alƙawarin cewa 2023 za a bawa kudu, shugabancin kasa ya koma kudu.
"Amma dai, siyasa ne. Ya kamata mu zauna mu tattauna ne kan wannan batun a tsakanin mu, mu yan siyasa.
"Wannan kalmar da wasu ke furtawa na cewa dole mulki ya koma kudu, ina son su dena amfani da kalmar dole."
Yankin mu ya kamata ya fitar da shugaban kasa na gaba, Gwamnonin Kudu
A wani labarin daban, Gwamnonin jihohin kudancin Nigeria 17 sun amince kan cewa shugaban kasar Nigeria na gaba a shekarar 2023 ya kamata ya fito daga yankinsu ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na dauke ne cikin sakon bayan taro da kungiyar gwamnonin kudun ta fitar bayan taron ta da aka yi a gidan gwamnatin Legas da ke Alausa, ranar Litinin.
Daily Trust ta ruwaito cewa sun kuma cimma matsayar cewa ya kamata a rika kama-kama ne tsakanin kudu da arewa wurin zaben shugaban kasar.
Asali: Legit.ng