UTME: Iyaye sun roke ni da in dafawa ’yayansu - Shugaban hukumar JAMB

UTME: Iyaye sun roke ni da in dafawa ’yayansu - Shugaban hukumar JAMB

  • Shugaban hukumar JAMB ya ce hukumar tana fuskantar kalubalen satar jarrabawa na dalibai da rashin da’a daga makarantu
  • Ya ce akwai iyayen da ke kiran sa da nufin ya taimaka ‘ya’yansu su ci jarrabawar
  • Ya nunar da cewa amfani da lambar NIN ta taimaka wa hukumar wajen bankado masu rajistar bogi

Shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, JAMB, Ishaq Oloyede ta ce satar jarrabawa da kuma rashin da’a sune manyan kalubalen da ke ci wa hukumar tuwo a kwarya.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, shugaban ya yi magana a ranar Litinin lokacin da mambobin kwamitin majalisar dattijai kan ilimin firamare da sakandare suka ziyarci hedikwatar hukumar da ke Bwari, Abuja.

Oloyede ya ce akasarin kalubalen sun shafi iyaye ne da ke kokarin yin coge ga tsarin, ta kowace hanya, don shigar da ‘ya’yansu makarantu, ba tare da la’akari da kokarinsu ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Oloyede ya ce:

"Kalubalen da muke fuskanta shi ne na satar jarrabawa, musamman dangane da iyayen da suke kira na da zimmar in dafawa 'yan uwansu ko yaransu ko ta halin kaka."
“Akwai kuma rashin da’a daga manyan makarantun da suke daukar dalibai ta hanyar da ta ci karo da ka’idojin da manufofin Gwamnatin Tarayya kamar yadda Ma’aikatar Ilimi ta ba da umarni.
“A karshen lamarin, bayan sun dauki daliban ta wannan hanyar, suna matsa lamba ga dalibai a lokacin da suka zo kammala karatun da su dawo gare mu domin abin da suke kira daidaita musu bayanansu.
Har ila yau muna da irin wannan kalubalen daga wasu bangarori masu zaman kansu da kuma cibiyoyin rubuta jarrabawar na Kwamfuta (CBT) sai dai su ma muna matukar kokarin magance su.”

DUBA NAN: Yadda zamu ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Osinbajo

Shugaban hukumar JAMB
UTME: Iyaye sun roke ni da in dafa wa’yayansu - Shugaban hukumar JAMB Hoto: JAMB
Asali: Depositphotos

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun ceto wasu da aka sace ciki har da dalibin makarantar Bethel

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Shugaban hukumar ya ce adadin wadanda suka yi rajistar a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare na shekarar 2021 (UTME) bai kai miliyan daya da dubu dari hudu ba, adadin da ya yi kasa idan aka kwatanta da miliyan 2.2 da suka zana jarrabawar a shekarar 2020.

Ya ce, duk da haka, tilasta amfani da lambar zama dan kasa ta NIN ya taimaka wa hukumar wajen dakile wadansu bata-gari da ake samu a yayin rajistar UTME.

Ya ce a lokacin zana jarabawar ta 2021, kalubalen hukumar ya koma kan jami’an tsaron da ke aiki a wasu cibiyoyin, wadanda ya ce ana zargin sun yi ta shigo da masu zana jarrabawar na bogi zuwa cikin zaurukan zana jarabawar.

Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

Kara karanta wannan

COVID-19: Yadda Najeriya ta kunyata masana - Aregbesola

Kwamitin ilimi na majalisar dattijan Najeriya, a ranar Talata, ya bayyana cewa zai yi garambawul a wasu dokokin hukumar JAMB, domin maida shekara 16 mafi ƙarancin shekarun ɗalibin da zai zauna jarabawar share fagen shiga manyan makarantu UTME.

Kwamitin ya ƙara da cewa duk wani ɗalibi da bai kai shekara 16 ba, bai kamata a bashi gurbin shiga jami'a ba domin shekaru na taka rawa wajen karatun ɗalibai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng