Bayan shekaru biyu da zabe, Buhari ya bayyana abin da ya sa APC ta rasa wasu jihohi a 2019

Bayan shekaru biyu da zabe, Buhari ya bayyana abin da ya sa APC ta rasa wasu jihohi a 2019

  • Shugaban kasa ya hadu da Gwamnonin da suka sauya-sheka zuwa APC
  • Muhammadu Buhari ya ji dadin karbar Ben Ayade da Bello Matawalle
  • Shugaban Najeriyar ya ce da gangan ne APC ta rasa wasu jihohi a 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi karin-bayani a kan abin da ya jawo wa jam’iyyarsa ta APC mai mulki rasa jihohi masu yawa a zaben 2019.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban kasar ya na cewa jam’iyyar APC ta sha kashi a wasu jihohi ne saboda gwamnatinsa ta nuna za ta iya jure wa adawa.

Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wannan jawabi ne jiya a fadar shugaban kasa yayin da ya karbi bakuncin gwamnonin jihar Zamfara da na Kuros Riba.

KU KARANTA: APC ta dakatar da zaben shugabanni na kasa

A ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, 2021, gwamna Bello Matawalle da takwaransa, Ben Ayade suka ziyarci shugaban kasar, bayan komawarsu jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

APC ta na neman maimaita kuskuren da ta yi a 2019 a zaben sabon Gwamnan Anambra

Kamar yadda rahoton ya nuna, shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni da Atiku Bagudu da Muhammed Badaru Abubakar ne su ka yi masu rakiya.

“Ina taya ka murna da ku dawo jam’iyyarmu mai daraja. Mun rasa jihohi da dama a zaben da ya wuce, wanda ba a san jam’iyya mai mulki da haka ba.”
“Mun yi wannan ne domin mu nuna wa Duniya cewa muna da juriyar adawa. Mu nuna cewa lallai mun yarda da zabin da daidaikun mutane suke da shi.”

KU KARANTA: Zaben Anambra: Shugabannin APC sun gagara sasanta rikicin ‘Yan takara

Buhari da manyan APC
Buhari da sababbin shiga APC Hoto: @FemiAdesina
Asali: Facebook
“Mun jajirce a kan girmama abin da mutanen mu su ke so. Shiyasa mu ka dage kan ayi zaben gaskiya da adalci.”
"Dole shugabanni su nuna gaskiya, kuma su girma mabiyansu.”

Shugaban kasar ya fitar da jawabi ta bakin hadiminsa, Femi Adesina, ya na cewa wannan lokaci ya na cikin lokutan da jam’iyyarsu ta APC ta fi kowane farin ciki.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

A baya kun samu rahoton cewa jam’iyyar APC ta ruguza daukacin shugabanninta na jihar Zamfara saboda shigowar gwamna Bello Matawalle cikin jam'iyyar.

Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa suna ganin ba a isa a taba masu shugabanni ba. Amma duk da haka kwamitin rikon kwarya ya nada wasu sababbin shugabannin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng