Gwamnatin Buhari ta soke kwangilar jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri inji Amaechi

Gwamnatin Buhari ta soke kwangilar jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri inji Amaechi

  • Gwamnatin Tarayya ta bada kwangilar gyara titin jirgin Fatakwal zuwa Maiduguri
  • Rotimi Amaechi yace an karbe wannan kwangila saboda rashin kwarewa kan aiki
  • Ministan yace za a nemi wani kamfani da ya kware sosai, sai a ba shi wannan aikin

Gwamnatin tarayya ta karbe kwangilar gyaran titin jirgin kasan da ta bada daga garin Fatawakal, jihar Ribas, zuwa babban birnin Maiduguri na jihar Borno.

Jaridar Leadership ta kawo rahoto a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, 2021, cewa an soke wannan kwangila, za a nemi wani sabon kamfanin da za a ba aikin.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Ministan sufuri na kasa, Chibuike Rotimi Amaechi, ya dage a kan cewa kamfanonin gida su kara kware wa a wajen aiki.

KU KARANTA: Wani jirgin kasa ya yi hadari a Zaria

Rotimi Amaechi ya ce sai ‘yan kwangilan Najeriya sun san aiki da kyau kafin a ba su kwangilar dogo.

Kara karanta wannan

Calabria: Hotunan gari a Italy da zasu bada N13.6m ga masu son komawa da zama

Mai girma Ministan ya yi bayani a kan abin da ya sa aka soke yarjejeniyar da aka shiga a baya, aka kuma shirya sake bada kwangilar ga wani kamfani dabam.

Ministan ya ce neman kamfanonin ‘yan kwangilan da ake yi domin a ba su wannan namijin aiki ba zai yiwu ba, dalili kuwa mafi yawansu ba su san kan aikin ba.

Da yake magana a karshen makon da ya wuce, jaridar ta ce Rotimi Amaechi yace ya na goyon baya a rika ba mutanen gida aiki domin a farfado da tattalin kasar.

Gwamnatin Buhari ta soke kwangilar jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri inji Amaechi
Wani jirgin kasa a Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: An dauki tsawon sa’o’i 3 a jeji, jirgin kasan Najeriya ya tsaya a hanya

“Ya na da kyau mu rika sayen kayanmu na Najeriya, yin haka zai taimaka wa ‘yan kasuwan gida, ta haka ne kurum za a zaburar da tattalin arzikin kasa.”
“Ina cikin masu mara wa Injiniyoyi da ‘Yan kwangilan Najeriya baya, mun yi kokarin aiki da manyan kwararru a harkar kere-kere.”

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, an kama wanda ya kitsa kisar gillar da aka yi wa Shugaba Moise

“Mun nemi wadanda su kayi shekaru biyar kan wannan aikin, sai kurum a dauki hotunan ayyukan wasu, a tattara, a kawo mana, saboda haka ba su cancanta ba.”

Hon. Amaechi ya ce kamfanin da za su iya wannan aiki su ne suke kula da ayyukan dogon Legas-Ibadan, Abuja-Kaduna da kuma aikin jirgin kasan Warri-Itakpe.

A shekarar 2018 ne shahararren kamfanin nan na kasar Amurka watau General Electronics ya rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta zuba jari a Najeriya.

Kamfanin zai inganta harkar sufurin jirgin kasa a Najeriya tare da hadin guiwar gwamnatin tarayya domin a samu saukin zirga-zirga a fadin jihohin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel