An sallami manyan ma’aikata 2 daga aiki saboda sun fara binciken Atiku da Bola Tinubu

An sallami manyan ma’aikata 2 daga aiki saboda sun fara binciken Atiku da Bola Tinubu

  • Nigeria Financial Intelligence Unit ta kori wasu manyan ma’aikatanta biyu
  • Wadannan ma’aikata sun debo wa kansu ruwan dafa kansu da wasu bincike
  • Mohammed Mustapha da Fehintola Salisu na kokarin binciken wasu manya

Hukumar nan ta Nigeria Financial Intelligence Unit, ta fatattaki ma’aikatanta da ta dakatar kwanakin baya a kan binciken Atiku Abubakar da Bola Tinubu.

Jaridar Premium Times ta samu labari cewa shugaban NFIU na kasa, Modibbo Tukur, ya sanar da wadannan ma’aikata biyu a takarda cewa an sallame su daga aiki.

Mohammed Mustapha da Fehintola Salisu sun rasa aikinsu

Malam Modibbo Tukur ya rubuta wa ma’aikatan wasikun sallama a ranar 29 ga watan Yuni, 2021.

KU KARANTA: NFIU ta dakatar da masu binciken Bola Tinubu da Atiku Abubakar

Mohammed Mustapha da Fehintola Salisu wadanda sun kai matsayin mataimakin darekta sun rasa aikin su ne saboda sun kikiri Bola Tinubu da Atiku Abubakar.

Shugaban NFIU, Modibbo Tukur ya zargi ma’aikatan da wasu laifin, amma ana tunanin babban abin da ya sa aka kore su, shi ne sun taba wadannan ‘yan siyasan.

Kara karanta wannan

Kotu za ta bada umurni a kamo mata tsohuwar Ministan Nigeria da ake zargi da handame dukiyar al'umma

Laifin da ma’aikatan su ka aikata a hukumar NFIU

NFIU ta na zargin Mohammed Mustapha da rubuta wa shugaban ‘yan sanda da hukumar EFCC takarda, ya na binciken Atiku, ba tare da umarnin Modibbo Tukur ba.

Tukur ya ce wannan aiki da Mustapha ya kinkimo ba ya cikin wanda aka ba sashensa dama ya gudanar. Haka zalika wannan shi ne laifin da Fehintola Salisu ta yi.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC za ta wargaje idan Buhari ya tafi - Sule Lamido

Atiku da Bola Tinubu
Manyan ‘Yan siyasa, Atiku da Tinubu Hoto: www.thewillnigeria.com
Asali: UGC

Rahoton ya ce Fehintola Salisu ta rubuta takarda, ta na bukatar ayi bincike a kan tsohon mataimakin shugaban kasar, har lamarin ya fita daga hukumar NFIU.

Har ila yau Tukur ya na zargin Mustapha da aika takarda zuwa Amurka ya na binciken jigon APC, Bola Tinubu, saboda wata tsohuwar shari’a da ya taba da yi da CCB.

Wannan ya sa aka dakatar da jami’an daga aiki a baya, amma ana zargin duk da an dakatar da su, Mustapha ya cigaba da karbar albashi, wanda hakan ma wani laifi ne.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Wadanda suka sace Sarkin Kajuru sun yi magana, sun ce a kawo Miliyan 200

A karshen makon jiya ne aka ji tsohon Ministan harkar noman Najeriya, Akinwumi Adesina, ya fasa kwai, ya ce Atiku Abubakar ya koma makaranta tsofai-tsofai da shi.

Tun a shekarar 1960 Atiku Abubakar ya shiga sakandare, ya yi diflomarsa a jami'ar ABU tun 1967. Sai ga shi kwanan nan an ji cewa ya na yin digirgir a wata jami'ar Ingila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel