Labari mai zafi: Wadanda suka sace Sarkin Kajuru sun yi magana, sun ce a kawo Miliyan 200

Labari mai zafi: Wadanda suka sace Sarkin Kajuru sun yi magana, sun ce a kawo Miliyan 200

  • Wadanda suka dauke Sarkin Kujeru da mutum 13 sun tuntubi mutanensa
  • ‘Yan bindigan sun sa har Naira miliyan 200 a matsayin kudin da za a biya
  • Kakakin fadar Sarkin Kajuru ya ce suna neman alfarama a fito da Sarkin

Miyagun mutanen da su ka yi garkuwa da Mai martaba Sarkin Kujuru, Alhaji Alhassan Adamu, a jihar Kaduna, sun nemi a biya su kudin fansa.

'Yan bindiga sun ce a kawo Naira Miliyan 200

Rahotannin da mu ke samu daga jaridar Daily Trust sun tabbatar cewa ‘yan bindigan sun tuntubi iyalin mai martaba, sun nemi a ba su N200m.

A ranar Lahadi ne aka yi awon-gaba da Sarki Alhassan Adamu tare da wasu ‘yanuwansa da fadawansa, dazu ne aka fara tuntubar iyalansa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru a Kaduna

Channels TV ta bayyana cewa Mai magana da yawun bakin fadar Mai martaba Sarkin Kajuru, Dahiru Abubakar, ya tabbatar da wannan lamari.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru

Alhaji Dahiru Abubakar ya ce ‘yan bindigan sun bada tabbacin duka mutanen da aka dauke, suna nan lafiya kalau, babu wanda aka muzgunawa wa.

Mu na roko su fito da Mai martaba - Dahiru Abubakar

Kakakin masarautar ya ce su na rokon wadannan mutane su saki dattijon Sarkin mai shekaru fiye da 80 da ‘yanuwansa ba tare da an ba su wani abu ba.

Abubakar ya bayyana cewa sun bukaci a fito da Mai martaban ganin cewa bai da cikakken lafiya.

KU KARANTA: Yadda aka dauke Sarkin Kajuru da mutane 12 a kasarsa

'Yan bindiga
'Yan bindiga sun addabi Kaduna Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

A ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, 2021, Dahiru Abubakar, ya sanar da manema labarai wannan. Ana tunanin ba a dade da magana da ‘yan bindigan ba.

Mun fahimci cewa har yanzu ana kokarin shawo kan wadanda su ka yi awon-gaba da mai martaba, Adamu da wasu na-kusa shi, ba a cin ma matsaya ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sojoji sun bazama daji don ceto sarkin Kajuru da iyalansa daga 'yan bindiga

A baya kun ji cewa bayan sace ‘Yan makaranta da ake yawon yi a jihar Kaduna da kuma dauke Sarkin Kajuru, ana bin mutane gida a dauke su a yankin Zaria.

Matsalar rashin tsaro ya yi kamari a fadin jihar Kaduna, ana yawan yin garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel