A shekara 74, Atiku Abubakar ya koma gaban Malamai, ya na neman Digirgir a kasar Ingila
- Alhaji Atiku Abubakar ya ajiye tsufansa a gefe, ya koma daukar karatu
- Tsohon Mataimakin shugaban kasar ya na yin digirgir ya na shekara 74
- Akinwumi Adesina ya tona abin da Duniya ba ta sani ba a ranar Asabar
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya koma makaranta, inda yake yin karatun digirgir a jami’ar kasar waje.
Mutumin da ya bayyana cewa, Atiku Abubakar ya koma karatu shi ne shugaban bankin cigaban kasashen nahiyar Afrika, Dr. Akinwumi Adesina.
Kamar yadda PM News ta rahoto, kafin yanzu babu wanda ya san cewa Wazirin na Adamawa ya na karatu, sai da Akinwumi Adesina ya fasa kwai.
KU KARANTA: Masu zanga-zangar #BuhariMustGo da aka kama, sun tafi kotu
Akinwumi Adesina ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya na karatun digirgir (Masters) a bangaren ilmin huldar kasa-da-kasa a jami'ar Ingila.
Da yake bayani a wajen bikin yaye daliban jami’ar American University of Nigeria, Adesina bai iya bayyana makarantar da Atiku Abubakar ya shiga ba.
Tsohon Ministan harkar gonan ya yabi Atiku wanda shi ya kafa jami’ar nan da ake ji da ita, American University of Nigeria a Yola, jihar Adamawa.
Atiku mutum ne mai kwadayin karatu - Adesina
“Ya na son ilmi, kuma ta haka ne za a iya kawo gagarumin canji.”
KU KARANTA: Mutum miliyan biyu sun samu aiki ana fama da COVID-19 a Najeriya - Osibanjo
“Ina yi masa ba’a kwanan nan, sai na ke tambayarsa, meyasa a shekarunsa, ya tafi karatun digirgir a bangaren huldar kasa da kasa a Birtaniya.”
“Sai ya fada mani cewa ya na so ya samu digiri ne domin gano dalilan da ya sa ya aikata wasu abubuwan da ya yi a lokacin ya na gwamnati.”
Atiku Abubakar ya rike kujerar mataimakin shugaban kasa na shekaru takwas a gwamnatin Olusegun Obasanjo daga Mayun 1999 zuwa Mayun 2007.
A shekarar bara kun samu labarin yadda Hadiza El-Rufai ta yi wa Atiku Abubakar gyara a sakon ta’aziyyar da ya fitar na rasuwar Sheikh Ahmad Lemu.
Uwargidar gwamnan jihar Kadunan, Isma-El-Rufai ta nuna cewa wata kalma da Atiku Abubakar ya yi amfani da ita, sam ba ta nufin abin da yake tunani.
Asali: Legit.ng