APC ta na neman maimaita kuskuren da ta yi a 2019 a zaben sabon Gwamnan Anambra
- An samu sabani wajen gudanar da zaben tsaida ‘Dan takaran APC a Anambra
- Har yanzu Jam’iyya ta gagara shawo kan rikicin da ke tsakanin ‘Yan takararta
- Idan aka tafi a hakan, to APC za ta iya rasa kuri’u kamar yadda ta yi a Zamfara
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto game da zaben sabon gwamnan Anambra da za a gudanar inda ta bayyana cewa yakin neman zaben ya dauki zafi.
Manyan jam’iyyun APC, PDP da APGA ne ake ganin za su yi nasara a zaben na Nuwamban 2021, sai dai akwai irinsu jam’iyyar YPP da ta fara yin karfi.
Jam’iyyar APGA da PDP ne su ka fi farin jini a jihar Anambra, amma dukkansu suna fama da rikicin cikin gida iri-iri da ka iya kawo masa babban cikas.
KU KARANTA: Jam’iyya ta kori duka Shugabannin APC a jihar Zamfara
Ita ma jam’iyyar APC mai adawa ta na fuskantar irin wannan matsala bayan sakamakon zaben fitar da gwanin da ta shirya ya jawo mummunan sabani.
Kwamitin Dapo Abiodun ya bayyana Sanata Andy Uba a matsayin wanda zai rike wa APC tuta a zaben gwamnan da za ayi, hakan bai yi wa wasu daidai ba.
Cif George Moghalu ya ce jam’iyyar APC ba ta gudanar da zaben fitar da gwani ba, ya ce magudi kurum aka tafka, aka ce Sanata Andy Uba ne ya lashe tikitin
Paul Orajiaka da Edozie Madu, suna tare da Moghalu, sun ce ba su yarda da sakamakon zaben ba.
KU KARANTA: Mataimakin Gwamna ya na neman kujerar Matawalle
Wannan shi ne ra’ayin irinsu Johnbosco Onunkwo, Ben Etiaba, Amobi Nwaokafor, Chidozie Nwankwo, Geoffry Onyejegbu, da kuma Azuka Okwuosa.
Idan APC ta ki daukar mataki wajen gyara zaben fitar da gwanin da aka yi kwanaki, zai iya jawo mata matsala wajen shiga babban zabe da za ayi a Nuwamba.
Irin wannan kuskuren ne shugabannin jam’iyyar APC suka yi a 2018, a karshe aka yi watsi da kuri’un da ta samu a duka zabukan da aka shirya a Zamfara.
Idan za ku tuna Chris Ngige ya yi irin wannan korafi, ya yi kira ga kwamitin Dapo Abiodun tadakatar da zaben fitar da gwanin, amma ba a saurare shi ba.
Ministan kwadago ya bayyana cewa masu shirya zaben ba su hallara ba har dare ya yi, don haka 'ya 'yan APC su ka tafi gida ba tare da sun iya kada kuri'arsu ba.
Asali: Legit.ng