Sauya-shekar Gwamnan Zamfara ya na neman jawo danyen hargitsi a Jam’iyyar APC

Sauya-shekar Gwamnan Zamfara ya na neman jawo danyen hargitsi a Jam’iyyar APC

  • Tsohon Sanatan Zamfara ya soki dawowar Bello Matawalle zuwa Jam’iyyar APC
  • Kabiru Marafa ya yi hira a ARISE NewsNight, ya ce sauya-shekar ta sabawa doka
  • Sanatan ya na ganin APC ta haifi ‘Ya ‘yan shegu a Zamfara da wannan matakin

Kabiru Garba Marafa, daya daga cikin kusoshin jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ya sake yin magana a game da sauya-shekar gwamna Bello Matawalle.

Gidan talabijin na Arise News ya yi hira da Kabiru Marafa, inda ya yi tir da jawo gwamnan Zamfara da shugabannin APC su ka yi zuwa cikin jam’iyyarsu.

APC ba ta damar rike mukami tsakanin 2019 zuwa 2023 a Zamfara

A cewar Sanata Kabiru Marafa, sauya-shekar Mai girma Bello Matawalle zuwa APC ta saba wa hukuncin da kotun koli ta zartar a kan zaben Zamfara a 2019.

KU KARANTA: APC ta koma hannun Matawalle a Zamfara - Yariman Bakura

Tsohon ‘dan majalisar na jihar Zamfara ya ce kotu ta ce babu jam’iyyar APC a zaben da ya wuce a Zamfara, don haka bai kamata su rike kujeru kafin 2023 ba.

‘Dan siyasar yake cewa abin da zai sa APC ta samu wata kujera a jihar Zamfara shi ne idan har wanda yake kai ya mutu, ko ya yi murabus, ko dai an tsige shi.

“Kotu ta ce bai dace APC ta shiga takara a 2019, babu APC yanzu a Zamfara. To ina so a fada mani, mutumin da ba a hallice sa ba, zai iya haihuwar ‘ya ‘ya.”
Kabiru Marafa
Tsohon Sanatn Zamfara ta tsakiya, a Kabiru Marafa Hoto: www.guardian.ng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zaman Kwankwaso a PDP ya ki yiwuwa, ya na hangen komawa APC

“Wasa da hukuncin kotu da raina shari’a ne a ce APC ta na mulki. Mun hakura, mun rungumi kaddarar, APC ta bar mu a halin da mu ke, kar ta tono rigima.”

Za mu tabo Mai Mala Buni idan har ta kama

Jaridar This Day ta dauko wannan rahoto inda Sanatan ya ce idan ta kama za su kalubalanci halaccin gwamna Mai Mala Buni ya rike shugabancin jam’iyya.

A matsayinsa na gwamna, Sanata Marafa ya ce dokar APC ba ta ba shi dama ya shugabanci APC ba.

“APC ta kyale abubuwa yadda su ke. Kwamitin Mala Buni bai da ikon da zai dauki wannan mataki (na ruguje shugabannin jam’iyyar APC a jihar Zamfara.”

Idan mu ka koma siyasar Kudu, za mu ji cewa Jam’iyyar PDP ta bi hannun kotu, ta na so a tsige Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma daga kan karagar mulki.

Lauyan PDP ya je kotun koli ya na cewa bai dace Hope Uzodinma ya zama Gwamna ba. Hujjar jam'iyyar adawar ita ce Sanata Uzodinma bai da Jam’iyya a zaben 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel