PDP ta dauko Lauyan da zai karbo mata duka kujerun wadanda su ka koma APC a Zamfara

PDP ta dauko Lauyan da zai karbo mata duka kujerun wadanda su ka koma APC a Zamfara

  • Kanu Agabi zai tsayawa Jam’iyyar PDP, ta yi shari’a da ‘Ya ‘yan APC a Zamfara
  • Jam’iyyar adawar ta na kalubalantar komawa APC da ‘Yan siyasar jihar su ka yi
  • Tsohon Ministan zai jagoranci shari’a da Bello Matawalle da ‘Yan Majalisan APC

Bayan gwamna Bello Matawalle ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP, ya koma APC, tsohuwar jam’iyyarsa ta zabi ta shigar da karar shi zuwa kotu.

Jam’iyyar PDP ta kammala shirin zuwa kotu

Jaridar This Day ta tabbatar da cewa majalisar aiwatar wa ta NWC ta PDP, ta zabi Godwin Kanu-Agabi a matsayin lauyan da zai shigar mata da kara.

Rahotanni sun bayyana tsohon Ministan shari’a na kasar zai kalubalanci sauya-shekar da mafi yawan masu rike da mukamai a jihar Zamfara su ka yi.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya yi karin haske kan barin PDP

Jam’iyyar PDP za ta kai kara a gaban kotun tarayya a cikin makon nan, ta na mai neman a karbe mukaman wadannan ‘yan siyasan da su ka shiga APC.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle: APC ta dauki matakin da zai harzuka Jiga-jigan Jam'iyya a Zamfara

Wata majiya daga PDP ta ce jam’iyyar za ta kafa hujja da sashe na 221 na kundin tsarin mulkin kasa da ya ce jam’iyya ce ta ke shiga takara ba mutum.

Haka kotu ta zartar a shari’ar James Faleke da hukumar INEC a shekarar 2016 a dambarwar zaben gwamnan Kogi, don haka PDP ta ke ganin alamun nasara.

Lauyoyin da PDP za ta dauka za su kuma dogara da sassa na 179 da 181 na kundin tsarin mulki domin a tsige masu mulkin da su ka sauya-sheka a jihar.

KU KARANTA: Shugabannin PDP su yi murabus saboda ana komawa APC - Kwewum

Gwamnan Zamfara
Gwamna Bello Matawalle Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kanu Agabi

Kanu Agabi babban lauya ne da ya rike Ministan shari’a a gwamnatin Olusegun Obasanjo. The Cable ta ce ya na cikin wadanda su ka ceci Bukola Saraki.

Agabi ne ya dauki hayar Lauyoyi 106 zuwa kotu domin kare tsohon shugaban majalisar dattawan a lokacin shari’arsa da hukumar CCT, kuma ya samu nasara.

Kara karanta wannan

APC ta dage babban taron jam’iyyar na kasa har ila masha Allah

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa bayan gwamna Bello Matawalle, akwai Sanatoci uku, ‘yan majalisar dokoki 23 da na tarayya shida da su ka koma APC.

A baya kun ji Salihu Usman Zurmi ne kadai ya ki sauya-sheka a cikin 'yan majalisar dokokin Zamfara, ya ce koyarwar addini ta sa ya ki yarda shiga APC.

‘Dan Majalisar ya ce PDP ta gama yi masa komai, tun da ta ba shi takara, don haka ya nuna ba zai butulce mata ba a matsayinsa na wanda ya san ilmin addini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel