Masu zanga-zangar ‘BuhariMustGo’ da aka cafke, sun kai karar Minista da Shugaban DSS a kotu
- Matasan da aka kama da rigunan BuhariMustGo sun dumfari kotu a Abuja
- Lauyoyin wadannan mutane sun bukaci Alkali ya bada umarni a fito da su
- Matasan sun ce tsare su da ake yi, ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasa
Wasu matasa biyar da jami’an tsaron DSS su ka tsare a makon da ya wuce saboda suna dauke da rigunan #BuhariMustGo, sun kai karar hukuma a kotu.
Jaridar Punch ta ce wadannan Bayin Allah sun shigar da kara ne a wani babban kotun tarayya da ke garin Abuja, kwanaki kusan hudu bayan yin ram da su.
Ma’aikatan DSS masu fararen kaya sun kama wadannan mutane ne a cocin Dunamis Gospel na Abuja, kamar yadda jaridar Head Topics ta bayyana a yau.
KU KARANTA: Gamayyar kungiyar mata ta yi karar Shugaban kasa da AGF a kotu
Karar da Lauyoyi su ka kai a kotun tarayya
Kamar yadda rahoton ya zo mana dazu, matasan sun hada da babban limamin wannan coci da ke birnin tarayya, Fasto Paul Enenche a karar da su ka shigar.
Henry Nwodo, Victor Udoka, Emmanuel Larry, Samuel Gabriel da Ben Manasseh sun shigar da mabanbantan kara ne a gaban Alkali ta bakin lauyoyinsu.
Wadannan matasan su na rokon Alkali ya hana jami’an DSS da sauran wadanda su ke kara a kotu, damar taba su, da sunan an keta hakkinsu na ‘Yan adam.
Lauyoyin da su ka tsaya wa matasan su na ikirarin cewa kowa ya na da damar da zai bi addinin da ya ke sha'awa, da kuma abin da ya so a doka da tsarin mulki.
KU KARANTA: An kyauta da aka cafke Nnmadi Kanu - Buhari
Tsare mu ya saba doka da tsarin mulki
Sassa na 35, 388, 39, da 42 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 sun ba kowane ‘dan kasa ikon ya zabi addinin da zai bi, da ra’ayin da ya ke so.
Sannan matasan sun dogara da dokar kasa ta 2004 da sassa na 1, 2, 6, 8 da na 9 na dokar kare hakkin Bil Adama a Afrika da ta halasta masu abin da su ka yi.
Wadanda aka maka a kotu su ne hukumar DSS, Fasto Paul Enenche, shugaban DSS, Yusuf Bichi, da kuma Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami SAN.
A shari’o’in masu lamba FHC/ABJ/CS/631/2021, FHC/ABJ/CS/636/2021, FHC/ABJ/CS/637/2021, FHC/ABJ/CS/638/2021 da FHC/ABJ/CS/639/2021, an roki a fito da su.
Wani lauya mai kare hakkin Bil Adama a Najeriya, ya ce sun kai kara gaban Alkali, sun bukaci a saki wasu mutane 13 na kusa da Sunday Igboho da aka kama.
Kwanakin baya DSS su ka dura gidan wannan mutum, su ka yi gaba da mutane, da wasu makamai.
Asali: Legit.ng