Manufofin Gwamnatin Buhari sun ba mutum miliyan biyu abin yi cikin shekara 1 inji Osinbajo
- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yabi tattalin arzikin Najeriya
- Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnati ta tsare ayyuka sama da miliyan biyu
- Tattalin arzikin Najeriya bai girgiza sakamakon annobar cutar COVID-19 ba
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta sama wa mutane har fiye da miliyan biyu hanyar cin abinci a Najeriya.
Mai girma Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa mutane da-dama sun samu aiki ne ta sanadiyyar tsarin tattalin arzikin da su ka shigo da shi.
Shirin Economic Sustainability Plan
A cewar Mataimakin shugaban Najeriyar, wannan shiri na Economic Sustainability Plan (ESP), ya taimaka.
KU KARANTA: Ana rikici a kan mutum 774, 000 da za a ba aikin kwadago
Jaridar The Cable ta ce Yemi Osinbajo ya yi wannan ikirari a lokacin da aka yi wani taro da kwamitin ESP ta yanar gizo a ranar 5 ga watan Yuli, 2021.
An kawo tsarin ESP ne a watan Yunin 2020 domin a taimaka wa al’umma da gudumuwar kudi da nufin a rage radadin da annobar COVID-19 ta jefa mutane.
A cikin shekara daya da kawo wannan shiri na Economic Sustainability Plan, ya inganta tattalin arzikin marasa karfi, marasa galihu, da kananan ‘yan kasuwa.
“Mun gode wa tsarin gwamnatin tarayya na bada tallafin COVID-19, tattalin arzikin Najeriya bai sukurkuce ba, an samar da sababbin ayyuka kuma an tsare wadanda ake da su da har sama da miliyan biyu.”
KU KARANTA: Zabukan 2023 na fuskantar barazana saboda rashin tsaro - FCDO
Rahoton ya ce duk da irin nasarorin da aka samu, gwamnatin tarayya a karkashin Muhammadu Buhari, sai dai ba a iya kashe Naira tiriliyan 2.3 da ta yi niyya ba.
Farfesa Yemi Osinbajo ya ce a watan Mayu, an fitar da Naira miliyan 500, wanda hakan ya tallafa wa rayuwar miliyoyin mutane a lokacin da ake cikin halin matsi.
“An samar kuma an tsare ayyuka 2,100,021, alkaluma sun nuna an ba mutane miliyan 1.3 abin yi ta hanyar tsarin MSMEs da kudin da ake raba wa kai-tsaye.”
Cikin yadda aka ba mutane hanyar samun na abinci shi ne fito da tsarin daukar ma’aikata 774, 000 da aka dauka, sannan an ba mutane 26, 021 aiki daga kwangiloli.
Mun ji cewa Amurka, Ingila, Faransa da sauran kasashen da ke karkashin kungiyar G7, za su yi karo-karo, su ba gwamnatin Najeriya gudumuwar fam Dala miliyan 382.
Catriona Laing ta ce mutane miliyan 8 da doriya su ke bukatar a kawo masa dauki a Arewa ta gabas.
Asali: Legit.ng