Hadiza El-Rufai ta yi wa Atiku gyara a sakon ta’aziyyar Marigayi Sheikh Lemu

Hadiza El-Rufai ta yi wa Atiku gyara a sakon ta’aziyyar Marigayi Sheikh Lemu

- An ci gyaran Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar a sakon ta’aziyyar Ahmed Lemu

- Hadiza El-Rufai ta yi wa tsohon Mataimakin shugaban kasar gyara a shafin Twitter

- Uwargidar Gwamnan ta nuna akwai kure a wata kalma da Atiku ya yi amfani da ita

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya na cikin wadanda su ka fara aika ta’aziyyar Marigayi Sheikh Ahmed Lemu wanda ya rasu jiya.

A sakon ta’aziyyar ‘dan siyasar ya rubuta: “Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un! Ahmed Lemu, OFR fitaccen Alkali ne, malamin addini, mai tausayin al’umma kuma mai taimakon marasa karfi.”

“Mutuwarsa a lokacin da wadanda ya yi wa bauta har da Najeriya su ke bukatar shawararsa, babbar asara ce. Za a yi kewansa matuka.” Inji Atiku a Twitter.

A jawabin na sa, Atiku Abubakar ya bayyana marigayin da ‘Humanist’, amma Hadiza Isma-El-Rufai ta ci gyaransa, ta nuna masa cewa ya yi kuskure.

KU KARANTA: Abubuwa 10 da ba ka sani ba game da Sheikh Ahmad Lemu

Uwargidar gwamnan na jihar Kaduna, Hadiza Isma-El-Rufai ta nuna Kalmar HUMANIST, abin da ta ke nufi dabam da abin da Atiku Abubakar ya ke tunani.

Hadiza El-Rufai ta ce HUMANIST ya nufin mutumin da ya yi imani da akidar nan ta humanism.

Sannan mai dakin tsohon Ministan ta ce abin da Kalmar HUMANISM ta ke nufi shi ne mutumin da ya yi imani da karfin ikon Bil Adama a maimakon wani karfin Ubangiji ko halittar boye.

Da alamu abin da Waziri Atiku Abubaka yake nufi shi ne Ahmed Lemu ya kasance mai tausayin jama’a da yin abin da al’umma za su amfana.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Tarayya za ta haramta wasu barin Najeriya

Hadiza El-Rufai ta yi wa Atiku gyara a sakon ta’aziyyar Marigayi Sheikh Lemu
Sarkin Saudi da Marigayi Sheikh Lemu Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Amma wasu masana su na ganin cewa Atiku bai yi kuskure ba, domin Kalmar na da wata ma’ana. Marigayi Lemu har ya mutu, babban malami ne mai tsoron Allah.

Matar gwamnan shahararriyar marubuciya ce wanda ta ke koyawa jama’a harshen Ingilishi a Twitter.

A karshen makon nan ne ku ka ji cewa Allah ya yi wa shahararren malamin nan na addinin Musulunci da ke Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu rasuwa.

Marigayin ya yiwa addinin Musulunci hidima sosai a lokacin da yake raye. Haka zalika Mai dakinsa mutumiyar kasar waje, Marigayiya Aisha Lemu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel