APC ta dage babban taron jam’iyyar na kasa har ila masha Allah
- Jam’iyyar APC ta dage gudanar da zabukan jam’iyyar daga matakin gunduma har zuwa na kasa har illa masha Allah
- Sanarwar dage taron ta fito ne cikin wata takardar da shugaba da kuma sakataren rikon jam’iyyar na kasa suka rattaba wa hannu
- A cewar Shugabancin za a sanar wa hukumar zabe ta kasa sabbin ranakun gudanar da zabukan
A yayin da take karbar mambobin wasu jam'iyyun siyasa zuwa cikin ta, jam'iyyar APC ta sanar da dage ranar gudanar da tarukan jam’iyyar tun daga mazabu zuwa matakin kasa har illa masha Allahu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jam’iyyar APCn mai mulki ta bayyana hakan ne a wata wasika da ta aika a ranar 6 ga watan Yuli, kuma ta aike wa Shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC).
Wasikar da shugaba kwamitin rikon Jam’iyyar, Gwamna Mai Mala Buni da sakataren riko, Sanata John James Akpanudoedehe suka sanya wa hannu, ta ce nan gaba za a sanarwa hukumar zaben sabon ranar da ta sanya, riwayar The Nation.
Sai dai Jam’iyyar APCn mai mulki ba ta yi bayani game da sababbin ranakun da za ta gudanar da babban taron jam’iyyar na da kuma sauran matakan ba.
DUBA NAN: Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
KU DUBA: A tarihin Najeriya, babu gwamnatin ta taba jin kan talakawa irin ta Buhari, Gwamna Masari
A baya da Jam’iyyar APC ta fitar da jadawalin yadda za ta gudanar da tarukan zaben shugabannin jam’iyyar.
Idan za a tuna, jam’iyyar mai mulki ta fitar da jadawalin yadda za ta gudanar da taronta daga matakin gundumomi zuwa na shiyya.
Sai dai ko a lokacin ma jadawalin, bai fayyace ranar gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa ba. An sanya gudanar da taron gunduma a ranar 10 ga watan Yuli, yayin da aka kayyade na kananan hukumomi a ranar 6 ga watan Agusta.
Ta kuma kara da cewa za a gudanar da taron jihohi a ranar 3 ga Satumba sannan na shiyyoyi a ranar 30 ga Satumba.
Manyan APC na damuwa da shigar manyan jigogin PDP jam'iyyar
A daya gefen kuma, jiga-jigan APC sun nuna damuwa kan sauya sheka da jiga-jigan Jam’iyyar PDP suke yi zuwa cikin Jam’iyyar APCn suna masu da’awar cewa hakan ba alheri ba ne ga jam’iyyar.
Mambobin Kwamitin Kasa na jam’iyyar na Kungiyoyin da ke goyon bayan Sanata Al-Makura wadanda suka nuna fargaba kan abin da shugabannin jam’iyyar ke ganin alheri ne ribibin shiga jam’iyyar, suka aika da korafin ga shugabancin jam’iyyar a karkashin Mai Mala Buni.
Kwamitin a cikin sanarwar ya shawarci Buni da ya binciki karfin himma da gaskiyar dabi’un sababbin mambobin, musamman wadanda suka fito daga jam'iyyar hamayya.
Asali: Legit.ng