Gwamnan Zamfara ya yi karin haske kan zargin ‘matsin lambar’ da aka yi masa ya bar PDP

Gwamnan Zamfara ya yi karin haske kan zargin ‘matsin lambar’ da aka yi masa ya bar PDP

  • Bello Matawalle ya ce babu wanda ya tilasta masa sauya-sheka daga PDP
  • Gwamnan na jihar Zamfara ya bayyana dalilin ficewarsa PDP zuwa APC
  • Mai girma gwamnan ya yi wannan bayani ne ta bakin mai ba shi shawara

Mai girma gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce ya koma jam’iyyar APC mai mullki ne saboda ya samar da hadin-kai a siyasar jiharsa.

Jaridar The Nation ta rahoto gwamnan ya na wannan bayani a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli, 2021.

Wani hadimin gwamnan, Yusuf Idris, ya fitar da jawabi, ya musanya labarin da ke yawo na cewa don dole gwamna Bello Matawalle ya bar jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya dawo da wasu Hadimai da ya sallama

“Sanannen abu ne cewa gwamna Matawalle ya na cikin shugabanni masu hikima a kasar nan, kuma ya shiga APC ne saboda ya karfafa hadin-kai a jiharsa.”
“Ya yi wannan ne da nufin kawo wa mutanen jiharsa (Zamfara).”

Mai magana da yawun bakin gwamnan ya ce Matawalle ya zabi ya shiga tafiyar APC ne saboda irin goyon bayan da yake samu daga Muhammadu Buhari.

Haka zalika, kamar yadda wannan jarida ta bayyana, Yusuf Idris ya bayyana cewa shugabannin APC na kasa sun damu da halin da jihar Zamfara ta ke ciki.

Bello Matawalle
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Abin da ya kai Matawalle Jam'iyyar APC

Mai taimaka wa gwamnan wajen yada labarai ya ce masu adawa da sauya-shekar Mai girma gwamna Bello Matawalle ne su ke yada labarai akasin na gaskiya.

“Shugaban kasa Buhari da gwamnonin APC su na tausaya wa halin da mutanen jihar suka shiga. Wannan ya karfafa gwiwar gwamnan, ya maida masu alherinsu.”
“Makasudin komawar gwamnan zuwa jam’iyya mai mulki bai wuce wannan ba. Duk wani rahoto da ake ji ba gaskiya ba ne, sharrin magauta ne da su ke adawa.”

Kun samu labari cewa daga mutane fiye da 20, jam'iyyar PDP ta koma ta na da mutum 1 a Majalisar dokokin jihar Zamfara, bayan da APC ta karbe mulki.

‘Dan jam'iyyar PDP daya ya rage a Majalisar jihar Zamfara bayan Gwamnan jihar ya sauya-sheka. Hon. Salihu Usman Zurmi ya ce ba zai yarda ya koma APC ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel