‘Dan Majalisa ya bukaci duk Shugabannin PDP su yi murabus saboda sun gagara hana komawa APC

‘Dan Majalisa ya bukaci duk Shugabannin PDP su yi murabus saboda sun gagara hana komawa APC

  • Sauya-shekan da ake ta yi zuwa APC ya na neman jawowa Uche Secondus matsala a PDP
  • Rimamnde Shawulu Kwewum ya rubuta wasika, ya na so ‘Yan Majalisar NWC su sauka
  • ‘Dan Majalisar Taraban ya na ganin Shugabannin PDP ba za su iya takawa APC burki ba

Daily Trust ta rahoto cewa wani ‘dan majalisa a Najeriya, Rimamnde Shawulu Kwewum, ya yi kira ga duka shugabannin PDP na kasa, da su ajiye aikinsu.

Honarabul Rimamnde Shawulu Kwewum mai wakiltar wani yanki na jihar Taraba a majalisar wakilan ya na cikin wadanda ba su tare da Prince Uche Secondus.

'Yan PDP su na tsere wa, su na shiga jam'iyyar APC

Rimamnde Kwewum ya rubuta budaddiyar wasika ga shugaban PDP na kasa a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli, 2021, inda ya ce jam’iyyarsu ta na rasa ‘ya ‘yanta.

KU KARANTA: "Kwankwaso bai shirin ficewa daga Jam’iyyar PDP ya koma APC"

‘Dan majalisar tarayyar ya koka game da yadda jam’iyyar hamayyar ta ke rasa tulin ‘ya ‘yanta zuwa APC mai mulki a karkashin jagorancin Uche Secondus.

Abin da wasikar Hon. Rimamnde Shawulu Kwewum ta ce:

“Kamar yadda ake tsammani, ’yan majalisar wakilai hudu na jihar Zamfara sun bada sanarwar fice wa daga jam’iyyar PDP, sun koma APC mai mulki.”
“Ba yadda aka saba ji a da ba, lokacin da marasa rinjaye da bangaren shugabannin PDP a majalisa, su kan yi surutu idan har an sauya-sheka, yanzu ko fitowa ba a ji wani ya yi ba, ko aka tada kura a kan sauya-shekar.”
“Shugabanmu, ina rubuta maka wannan wasika da takaici, da kuma ganin girman ofishinka, da karon kanka, babu wanda zai yi watsi da cigaban da ka kawo wa PDP.”

KU KARANTA: Wani ‘Dan Majalisar Ingila zai bijiro da batun Kanu a Birtaniya

Rimamnde Shawulu Kwewum
Hon. Rimamnde Shawulu Kwewum Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC
“PDP kamar yadda ka sani, ya kamata ta zama ta na wakiltar abin da mutanen Najeriya su ke buri, ya kamata ta rika taka wa abin da gwamnatin APC ta ke yi burki.”

An rahoto Hon. Kwewum ya na cewa kullum PDP kara rauni ta ke yi, ana samun baraka, ‘ya ‘yanta su na bin jirgin APC, hakan ya jawo cikas wajen yi wa APC adawa.

‘Dan adawar ya ce Talakawa sun fara ganin PDP ba ta da ikon karbe mulki daga hannun APC, don haka ya bukaci Secondus da sauran ‘Yan majalisar NWC su ajiye mukamansu.

Ku na da labari cewa ana rade-radi cewa matsa wa Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, aka yi, har ya koma APC da karfi-da yaji, wannan ne ra'ayin shugaban PDP na kasa.

Bello Matawalle ya musanya hakan, ya ce babu wanda ya tursasa masa wajen sauya-sheka zuwa Jam’iyyar APC. Gwamnan ya karyata wannan ne ta bakin wani hadiminsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel