Ayoyin Qur’ani 3 na yi aiki da su, na ki barin Jam'iyyar PDP inji ‘Dan Majalisar Zamfara

Ayoyin Qur’ani 3 na yi aiki da su, na ki barin Jam'iyyar PDP inji ‘Dan Majalisar Zamfara

  • Salihu Usman Zurmi ne kadai ya ki komawa APC a Majalisar Zamfara
  • Hon. Zurmi ya ce koyarwar addini ta sa ya ki yarda ya yi watsi da PDP
  • ‘Dan Majalisar ya ce PDP ta gama yi masa komai, tun da ta ba shi takara

Honarabul Salihu Usman Zurmi wanda ake kira Gurgu, shi kadai ne ya rage a cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a majalisar dokokin jihar Zamfara.

BBC Hausa ta yi hira da Salihu Usman Zurmi, domin jin abin da ya sa ya ki shiga jirgin APC.

Ganin irin alherin da PDP ta yi masa, ta ba shi tikitin shiga takara, don haka Salihu Usman Zurmi mai wakiltar mazabar Zurmi ta gabas, ya ki bin APC.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara, Matawalle, ya koma Jam'iyyar APC

Ba zan yi wa Allah butulci da ni'imar da ya yi mani ba

“Da yardar Allah a shekarar 2018, na nemi PDP ta aminta da ni, ta ba ni damar tsaya wa takara, Allah ya bada iko, ta amshi niyya ta, ta tsayar da ni a zaben 2019.”

A hirar, ‘Dan siyasar ya jawo ayoyi a Al-Qur’ani mai girma wadanda su ka sa ya zabi ya yi zamansa a PDP.

Hon. Salihu Usman Zurmi yake cewa a cikin littafin Al-Qur’ani, Madaukakin Sarki, Allah SWT ya na cewa idan bawa ya godewa ni’imarSa, zai kara masa.

A wani wuri kuma Allah (SWT) ya ce duk wanda ya dogara da Shi, zai samu mafita. A wata ayar kuma Allah (SWT) ya ce shi ne yake yin yadda duk ya so.

Gurgun ‘Dan Majalisar Zamfara
Hon. Salihu Usman Zurmi Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: UGC

KU KARANTA: Shigowar Gwamnan Zamfara APC ya na neman jawo rigima

Ganin haka ya sa Hon. Zurmi ya ce bai yarda ya butulce wa ni’imar da Allah ya yi masa a jam’iyyar PDP ba, hakan zai sa akasin ni'imar Allah ta zo masa.

“A ayoyin da na jawo maka, za ka gane cewa idan har na dogara a jam’iyyar PDP, Ubangiji zai iya yi mani wata baiwa fiye da wanda ya yi mani yanzu.”

A game da zargin cewa an ba shi wani abu domin ya cigaba da zama a PDP, ‘dan majalisar ya musanya wannan zargi, ya ce imani da Allah kurum ya yi.

A jiya ne Gwamnonin Kudu su ka yi wani zama na musamman a jihar Legas, inda su ka tsaida cewa daga yankinsu za a samu wanda zai zama Shugaban kasa.

Hakan ya na nufin burin irinsu Atiku Abubakar, Rabiu Kwannkwaso da sauransu, ya na fuskantar barazana idan aka kai takarar shugaban kasa zuwa Kudu a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng