Daga Karshe: An Sanya Ranar Mukabala Tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano

Daga Karshe: An Sanya Ranar Mukabala Tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano

  • Bayan kai ruwa rana da aka yi kan batun mukabalar Sheikh Abduljabbar, an sanya ranar da za a caccaka tsinke
  • Sheikh Abduljabbar da malaman Kano zasu zauna zaman mukabala a ranar Asabar mai zuwa, 10 ga watan Yuli
  • Gwamnatin jihar Kano ta amince da zaman ne domin sauraran hujjojin Sheikh Abduljabbar kan wasu batutuwa

Gwamnatin jihar Kano ta sanya ranar da za a caccaka mukabala tsakanin fitaccen malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malamai a jihar.

Kwamishinan harkokin addinai na jihar Muhammad Tahir Adamu wanda ake kira Baba Impossible ne ya bayyana haka ranar Alhamis a tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC.

Ya ce za a gudanar da mukabalar ce ranar Asabar 10 ga watan Yuli a Hukumar Shari'a dake birnin na Kano.

KARANTA WANNAN: Mafita: Matasan Katsina sun shirya horar da yadda za a fatattaki 'yan bindiga

Daga Karshe: An Sanya Ranar Mukabala Tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano
Sheikh Abduljabbar da Gwamna Ganduje | Hoto: legit.ng
Asali: Depositphotos

A cewarsa tuni ya mika takardar gayyatar yin mukabalar ga Abduljabbar da malaman da za su fafata da shi.

Kwamishinan ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan shugabannin zauren hadin kan malaman Kano suka zargi gwammatin jihar da "jan kafa" game da zaman tuhumar suka ce za su yi wa Sheikh Abduljabbar a kan zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa.

KARANTA WANNAN: Hakan jahilci ne: Minista Malami ya caccaki lauyan turai da ya kare Nnamdi Kanu

Da ma dai Sheikh Abduljabbar ya bayyana dakatarwar da gwamanatin ta yi masa na yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa "zalunci ne".

Kalli hotunan:

Daga Karshe: An Sanya Ranar Mukabala Tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano
Baba Impossible da wasu malaman Kano | Hoto: Ibrahim Disina
Asali: Facebook

Daga Karshe: An Sanya Ranar Mukabala Tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano
Baba Impossible da wasu malaman Kano | Hoto: Ibrahim Disina
Asali: UGC

Daga Karshe: An Sanya Ranar Mukabala Tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano
Wasikar da aka kai | Hoto: Ibrahim Disina
Asali: UGC

Abduljabbar bai kai a yi masa gangami ba, in ji Sheikh Khalil

A baya, shugaban malamai na arewa maso yamma, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanar da cewa kima da darajar Malam Abduljabbar Kabara basu kai ga malamai su yi masa gangamin taron dangi ba.

Sheikh Khalil ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da jaridar Leadership kan abinda ke faruwa tsakanin Abduljabbar da gwamnatin Kano.

Tun farko dai Ganduje ya haramtawa malamin yin wa'azi sakamakon zargin da da ake yi da bayar da wasu fatawoyi da suka sabawa koyarwar addini. Malamin yace rashin darajar ne yasa Sarki Musulmi ya ki tura wakilan JNI wurin mukabalar.

Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin jihar Kano a gaban kotu

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yaba da kokarin da sojojin Najeriya na Brigade 3 suka yi na tsare dajin Falgore da wasu sanannun gandun daji a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin 1 Division Nigerian Army na Kaduna, Ezindu Idimah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Kaduna.

Mista Idimah ya bayyana cewa tsare gandun dajin da sojoji suka yi ya hana masu aikata laifuka 'yancin aiwatar da munanan ayyukansu a ciki da kewayen wadannan dazukan.

A cewarsa, gwamna Ganduje ya yi wannan bayani ne lokacin da ya karbi bakuncin kwamandan 3 Brigade Nigerian Army, Brig-Gen. Sinyinah Nicodemus, wacce ta ziyarci Gwamnan a ranar 23 ga Yuni, a gidan Gwamnatin Kano.

Mista Idimah ya ruwaito Ganduje na danganta zaman lafiyar da aka samu a jihar ta Kano da irin hadin kan da ke akwai a tsakanin sojoji da 'yan uwansu jami'an tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel