Yanzu-Yanzu: El-Rufai ya bayyana dalilin cire yaronsa daga makarantar gwamnati

Yanzu-Yanzu: El-Rufai ya bayyana dalilin cire yaronsa daga makarantar gwamnati

  • Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ya cire dansa daga makarantar gwamnati ne saboda kasancewarsa na jefa sauran dalibai a hatsari
  • El-Rufai ya ce tun bayan da ya dauki matakin cewa ba zai biya kudin fansa ba a Kaduna, an kalla kungiyar yan bindiga uku sun yi yunkurin kai hari makarantar da nufin sace dansa
  • Gwamna El-Rufai ya ce hukumomin tsaro ne suka bashi shawarar cewa ya kamata a cire dansa a yanzu har zuwa wani lokaci da abubuwa za su daidaita

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana dalilin da yasa ya cire yaronsa mai shekaru bakwai, Al-Sadiq El-Rufai daga makarantar Kaduna Capital School a sirrance, Daily Trust ta ruwaito.

A shekarar da ta gabata ne gwamnan ya saka dansa a makarantar ta gwamnati amma daga bisani rahotanni suka nuna ya cire shi.

Gwamna Nasir El-Rufai da Dansa Al-Sadiq
Gwamna Nasir El-Rufai da Dansa Al-Sadiq a Kaduna Capital School. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A hirar da aka yi da shi da BBC Pidgin, El-Rufai ya ce yan bindiga na bibiyan dansa ne suyi garkuwa da shi saboda matakin da ya dauka ne dena biyan kudin fansa.

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari

A hirar da aka yi da shi, El-Rufai ya ce wannan ne karon farko da ya yi magana a kan lamarin.

Ya ce barin dansa a makarantar barazana ne ga sauran daliban a halin yanzu da ake fama da kallubalen tsaro sannan yan bindigan suna bibiyar dansa don sace shi.

Ya kara da cewa yarsa, Nesrin, ita ma an saka ta a makarantar a lokacin da ta cika shekaru shida.

Ya ce duk da cewa babu wata barazana ga Nesrin, an cire dukkan yaran biyu daga makarantar bisa shawarar hukumomin tsaro.

Ya ce:

"'Da na da kanwarsa dukkansu an saka su a makarantar saboda ita ma ta cika shekaru shida don haka muka yi mata rajista.
"Amma mun cire su daga makarantar na dan wani lokaci saboda mun kama a kalla kungiyoyi biyu da ke shirin su kai hari makarantar domin su yi garkuwa da yaro na.
"Bana tsammanin za su yi nasara domin an tanadar da isasun jami'an tsaro don gudun hakan ya faru amma kasancewarsu a makarantar na iya jefa sauran yara cikin hatsari.

KU KARANTA: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

"Ba mu san irin makaman da za su taho da su ba. Na dauki matakin ba zan biya kudin fansa ba kuma mun kama a kalla kungiyar yan bindiga uku da ke shirin zuwa Kaduna Capital School don sace 'da na su gani 'idan sun kama 'da na, zan ce ba zan biya kudin fansa ba?."

Ya bada tabbacin cewa ya cire dansa ne saboda kare sauran yaran da ke makarantar yana mai cewa ya gamsu da irin karatun da ake yi a makarantun gwamnatin jihar Kaduna shi yasa ya saka yaransa yana mai cewa yana da niyyar cigaba da tura yaransa makarantar gwamnati.

El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya yi matuƙar murnar kama Nnamdi Kanu

A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana farin cikinsa game da kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), News Wire ta ruwaito.

Ministan shari'a kuma Attoni Janar na kasa, Abubakar Malami (SAN), a ranar Talata, ya sanar yayin taron manema labarai cewa an kama Kanu tun a ranar Lahadi.

Da ya ke tsokaci a kan kamen lokacin da aka yi hira da shi a BBC Pidgin a ranar Juma'a, El-Rufai ya ce ya yi murna da kama Kanu saboda ya tsere bayan bashi beli sannan yana kirar Nigeria 'Zoo' wato gidan namun daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel