A tarihin Najeriya, babu gwamnatin ta taba jin kan talakawa irin ta Buhari, Gwamna Masari
- Babu gwamnatin da ta taba rayuwar talaka a tarihin Najeriya, cewar Masari
- Gwamnan ya shaida hakan ranar Alhamis a jiharsa
- Gwamnatin Buhari tace zata ciyar da dalibai milyan 14 nan da 2023
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shawarci wasu sassan Najeriya su rika yiwa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari adalci alal akalla.
Masari wanda ya siffanta gwamnatin Buhari a matsayin mafi jin kan talaka tun lokacin da aka kafa a Najeriya a 1914, ya ce yan Najeriya su godewa irin nasarorin da aka samu a tattalin arzikin tun 2015 da Buhari ya hau mulki duk da faduwar danyen mai a kasuwar duniya.
Masari ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron kaddamar da zaman mutanen da suka amfana da shirin ciyar da dalibai da gwamnatin tarayya ke yi a jihar Katsina, rahoton The Sun.
Masari yace:
"Wajibi ne muyi godiyan cewa tun lokacin da aka fara gwamnati a Najeriya, ba'a taba gwamnatin da ta taba rayuwar talakawa irin wannan gwamnati ba."
"Mutane kawai na magana ba tare da ganin irin kokarin da akeyi ba."
"Ko kun so, ko kun ki, shi (Buhari) ya kawo sauyi shugabanci ta yadda ko mutumin da bai taba sanin gwamnati ba yana amfana da ita.
Masari ya kara da cewa gwamnatin tarayya a kulli yaumin tana ciyar da akalla dalibai 800,000 a jihar Katsina, kuma wannan shiri na cin kudi sosai.
DUBA NAN: Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota
KU KARANTA: Abin mamaki yayin da wani mutum ya kara aure da kudin tallafin da kungiya ta ba shi domin kula da ’ya’yansa 7
Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya
Gwamnatin Tarayya za ta kara adadin daliban makarantun firamare da take ciyar wa daga miliyan tara zuwa miliyan 14 a karkashin shirinta na Ciyar da Daliban Makarantu na Kasa (NHGSFP).
Ministar Jin kai da Agaji, Hajiya Sadiya Farouk, ce ta bayyana hakan a lokacin da ta jagoranci wani ayari inda suka ziyarci Sakataren Gwamnatin Jihar Neja Ahmed Matane a ranar Juma’ah, rahoton Ptimes.
Ministar wacce mataimakin darakta a ma’aikatar Hezekiah Sunday, ta ce ayarin ya ziyarci jihar ce domin nazarin masu cin gajiyar shirin tare da duba yadda za a fadada shi.
Asali: Legit.ng