Ba za mu iya yin galaba kan ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da tsofaffin kayan aiki ba – Babban Hafsan Tsaro
- Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya ya ce lallai ne a bullo da sababbin dabaru da hanyoyin yakar ta’addanci
- Ya ce karfin sojin kadai ba zai samar da nasara ba
- A cewarsa rundunar sojin tana fama da yaki da ‘yan ta’adda daban daban a ‘yan shekarun nan
Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janal Lucky Irabor, ya ce tsofaffin kayan aiki da karfin soja kadai ba za su iya kawar da matsalolin tsaro kamar fashi da makami da satar mutane da kuma rikicin Boko Haram.
Da yake jawabi a wajen liyafar dare wanda aka shirya domin girmama daliban da suka kammala karatunsu na Babban Kwaleji karo na 43 na Kwalejin Sojoji a ranar Alhamis, Babban Hafsan ya ce sojoji sun bullo da sababbin dabaru da hanyoyin magance kalubalen tsaron kasar.
Ya ce samun galaba mai dorewa kan ta'addanci da tayar da kayar baya da sauran kalubalen tsaro na cikin gida na bukatar tsarin gwamnati baki daya ba kawai ta amfani da karfin soji ba.
Janar Irabor ya nunar da cewa shigar sojoji fama da aikin dakile barazanar tsaro a 'yan shekarun nan ya nuna bukatar lallai a samu sababbin dabaru da karfin aiki wajen magance barazanar da ta kunno kai.
Ya ci gaba da cewa:
"A saboda haka, muna fadada sababbin dabaru a bangaren leken asiri da sa ido, wadanda ke da matukar muhimmanci wajen kawar da 'yan ta'adda da masu tayar da kayar baya da sauran masu aikata laifi a cikin al'umma,"
KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido
DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo
Da yake jawabi ga daliban da suka kammala karatunsu wadanda suke a matsayin Manjo da manyan kwamandoji, Babban Hafsan ya ce:
“Kamar yadda kuka sani, yakin da muke fafatawa yana bukatar karfafa amfani da dabarun soja wadanda ba na dauri ba wadanda horonmu da koyarwarmu na shekarun baya ba su kunsar da su ba.
“A matsayinku na kananan shugabanni, dole ne ku yi amfani da horo da gogewarku wajen daukar mataki kan lokaci ga rundunoninku, musamman lokacin matsi.”
Ya ba da tabbacin cewa manyan hafsoshin soja na daukar matakai don magance barazanar tsaron.
Za a fitar da rahoton wucin-gadi kan musabbabin hatsarin jirgin tsohon Hafsan Sojan Kasa
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Ofishin Binciken Hadura, ya ce rahoton farko na musabbabin hatsarin jirgin saman soja wanda Babban Hafsan Sojan Kasa, Laftanal Janal Ibrahim Attahiru, da wadansu mutum 10 suka mutu a Kaduna a watan Mayun bana za a fitar da shi a makon gobe.
Babban Daraktan, ofishin Akin Olateru, ne ya bayyana hakan a lokacin da aka fitar da rahoton hatsarin jiragen sama guda takwas da ofishin ya fitar a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Asali: Legit.ng