Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

  • Wata mata ‘yar Arewacin Najeriya ta haifar da zazzafar muhawara a kafofin sada zumunta bayan ta koka kan halin da yankin ke ciki
  • Matar da ke cikin damuwa a sabon faifan bidiyon ta ce Arewa ita kurar baya ta kowane fanni sannan ga rashin ilimi
  • Ta soki ‘yan bokon yankin da ta ce suna amfana da duhun jahilcin mutanen yankin domin cim ma muradun kashin kai

Wata 'yar Najeriya ta haifar da zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta game da kalaman da ta yi kan halin da yankin Arewacin kasar ke ciki.

Matar a cikin faifan bidiyon da wani mai amfani da sunan @thetattleroom ya raba, ta yi tir da jahilci a Arewa, tana mai jaddada cewa yankinta na fuskantar koma baya a kowane fannin rayuwa.

Ta yi tur da halin rashin ilimi a yankin Arewacin kasar.

Matar wacce aka jiyo ta lokaci zuwa lokaci tana ingausa a cikin bidiyon ta kara da cewa yankin na Arewacin Najeriya yana fama da karancin ilimi.

Kara karanta wannan

Allah Ya kunyata Abduljabbar tun a duniya - Mallam Muhammad Rijiyar Lemo

Ta kuma yi kakkausar lafazi kan ‘yan bokon yankin wadanda ta ce suna cin gajiyar rashin ilimi a yankin wajen cim ma muradu na kashin kai.

Mune kurar baya a kowane bangare
Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo Hoto: @thetattleroom
Asali: Instagram

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da kalaman nata kamar haka:

Wani mai amfani da sunan @olajokes ya ce:

"Wannan shi ne bidiyo mafi kyau kuma na gaskiya daga ‘yan Arewa a cikin 'yan kwanakin nan .. Da yawa daga cikinsu sai dai su yi ta ikirarin abubuwa na tafiya daidai alhali ba haka lamarin yake ba."

Wani kuma @sheikhayates ya bayyana cewa:

"Uwargida ki yi taka tsantsan fa… kafin Buhari ya ce a sa a yi masa garkuwa da ke, koda yake na lullube ki da jinin Yesu."

Sai mai amfani da @_faithy_ola ya rubuta:

"Har yanzu sune suke hana ilimi a yankin Arewa tamkar dai laifi ne a samu ilimi."

Sai kuma @godsownayo ya yi tsokaci da cewa:

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun marawa Sanata Musa baya domin ya zama Shugabansu na kasa

"Ku ilimantar da Arewa ku ga yadda za a fahimci wannan shugabancin ya tabarbare. Jahilci ya munana kuma an yi amfani da addini a matsayin makamin juya akalar mutane, haba har yaushe?"

Kalli bidiyon:

A daya gefen kuma kafar labarai ta Legit.ng ta ruwaito a baya cewa wani mutum yana raki kan kwangilar aikin gina hanyar da aka yi a Jihar Edo.

Mutumin ya tabbatar da cewa titin bai samu ingantaccen aiki ba domin ana iya ganin sa yana cire kwalta da hannunsa domin nuna mummunan aikin da dan kwangilar ya yi.

A cewar Ajah, sababbin magudanan ruwan da aka gina ba su rodi a cikinsu sannan babu inganci a ginin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel