Za a fitar da rahoton wucin-gadi kan musabbabin hatsarin jirgin tsohon Hafsan Sojan Kasa
- Ofishin kula da hadurra zai fitar da rahoton farko kan musabbabin hatsarin jirgin da ya rutsa da tsohon Babban Hafsan Sojan
- Akasari yakan dauki wata 18 gabanin fitar da cikakken rahoton musabbabin hadari
- Sai rundunar sojin saman Najeriya ta ga dama za ta bayyana wa jama’a rahoton
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Ofishin Binciken Hadura, ya ce rahoton farko na musabbabin hatsarin jirgin saman soja wanda Babban Hafsan Sojan Kasa, Laftanal Janal Ibrahim Attahiru, da wadansu mutum 10 suka mutu a Kaduna a watan Mayun bana za a fitar da shi a makon gobe.
Babban Daraktan, ofishin Akin Olateru, ne ya bayyana hakan a lokacin da aka fitar da rahoton hatsarin jiragen sama guda takwas da ofishin ya fitar a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Sai dai ya kafe cewa ya rage wa rundunar sojin sama ta Najeriya ta yanke shawarar kan ko za ta bayyana wa jama’a sakamakon binciken da ke kunshe a cikin rahoton, yana mai jaddada cewa ba hurumin ofishin ba ne da fitar da irin wadannan bayanan.
Bayan faruwar hatsarin ne rundunar sojin saman ta nemi ofishin da ya jagoranci gudanar da binciken.
KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido
DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo
Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa har yanzu ofishin bai fitar da rahoto game da hatsarin ba a ranar Alhamis, Olateru ya ce,
“Binciken hadari na daukar lokaci; yakan dauki wata 18. Wannan da kuke magana a kansa, ku tuna cewa jirgin rundunar sojin sama ne, kuma wannan mummunan hadarin ya faru a filin jirgin saman farar hula.
“Don haka, ita rundunar sojin saman ta ga cewa za mu iya taimaka mata sannan ta bukaci da mu taimaka a gudanar da binciken, wanda yake gudana a halin yanzu, kuma ko rundunar sojin ta bayyana rahoton a fili ko akasin haka, wannan ba namu ba ne.
“Dalilin haka shi ne, baya daga cikin tsarin aikinmu. Amma a cikin makon gobe, rahoton wucin gadi zai bayyana."
Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru
Sojoji sun gudanar da addu'ar 40 ga marigayi COAS, Ibrahim Attahiru, tare da sauran manyan jami'ai 10, waɗanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hatsarin jirgi a Kaduna ranar 21 ga watan Mayu.
Yayi Jawabi a Gaban Kotu Addu'ar ta gudana ne bisa jagorancin daraktan al'amuran addinin musulunci na rundunar sojin ƙasa, Janar Shehu Mustapha.
Mustapha yayi addu'a ga rayukan mamatan su samu salama, kuma ya ƙara ta'aziyya ga iyalansu.
Asali: Legit.ng