Da duminsa: An sako dalibai da malaman da aka sace a Nuhu Bamalli Poly

Da duminsa: An sako dalibai da malaman da aka sace a Nuhu Bamalli Poly

  • Bayan kimanin wata guda hannun yan bindiga sun saki daliban NUBA Poly
  • Dalibai a makarantar sun tabbatar da samin wannan labari
  • Gwamnati ta tsaurara matakan tsaro a makarantar tun bayan harin da aka kai a baya

An sako dalibai shida da malamai biyu da yan bindiga suka sace a kwalejin fasahar Nuhu Bamalli dake Zariya jihar Kaduna kwanakin baya.

ChannelsTV ta rahoto cewa an sakesu ne da daren Alhamis.

Kakakin kwalejin fasahar, Abdullahi Shehu, wanda ya tabbatar da rahoton yace dalibai da malaman sun samu yanci ne bayan tattaunawa tsakanin 'yan uwansu da yan bindigan.

Amma bai bayyana ko an biya kudin fansa ko ba'a biya ba.

Ya kara da cewa anjima shugabannin makarantar zasu tarbi daliban a wurin da aka ajiyesu bayan sakesu.

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Da duminsa: An sako dalibai da malaman da aka sace a Nuhu Bamalli Poly
Da duminsa: An sako dalibai da malaman da aka sace a Nuhu Bamalli Poly Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Yan bindiga ranar 11 ga Yuni sun dira NUOBA Poly inda sukayi awon gaba da dalibai a dakunan kwanansu da kuma malamai a gidajensu.

Hakazalika sun hallaka dalibi daya lokacin harin.

Legit Hausa ta samu tattaunawa da dalibai a makarantar inda suka tabbatar da sakin abokan karatunsu.

Wata daliba mai suna Ummu Hani'i Liman, ta bayyana mana cewa:

"Mun shigo makaranta muka samu labarin. Mun ga hotunansu kuma mun ganesu amma basu dawo makaranta ba."
"Dukkansu aka saki, babu wanda ya rage."

Yayinda muka tambayeta kan shin an dauki matakan tsaron don kiyaye irin wannan abu a gaba, ta bayyana cewa lallai sun samu karin tsaro.

"Gaskiya an zuba Sojoji sosai da yan sanda kuma tun lokacin babu wata barazana," tace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel