Gwamnan Najeriya ya sauka daga motarsa da daddare, ya shiga sahun masu ba motoci hannu don hana cunkoso
- Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya ajiye mukaminsa a gefe domin sanya mutanensa cikin walwala
- Gwamnan dai ya sauka ne daga cikin motarsa sannan ya shiga cikin masu kula da zirga-zirgan ababen hawa domin saukaka wani cunkoso da ya hade
- Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba, 7 ga watan Yuli, yayinda ya tashi daga aiki
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya nuna kauna ga mutanen sa a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli, yayin da ya nuna abin da ake nufi da jagoranci.
Yayin da yake dawowa daga aiki, mutumin ya gamu da cunkoson ababen hawa a kusa da yankin Oke-Mosan na jihar. A cewarsa, cunkoson ya samo asali ne sakamakon ci gaba da aikin hanyar da ake yi a yankin.
KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen: Jacob Zuma da sauran tsoffin shugabannin Afirka da aka daure kurkuku
Ina so ababen hawa su yi zarya cikin walwala
Maimakon ya katse zirga-zirgar ababen hawa da karfin kujerarsa, sai ya sauko daga motarsa sannan ya hada hannu tare da masu kula da zirga-zirgar ababen hawa don sassauta lamarin.
KU KARANTA KUMA: Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili
Da yake wallafa hotunan aikinsa na sadaukarwa a Facebook, sakon da gwamnan ya wallafa ya ce:
"A kan hanyata ta dawowa ofis da yammacin yau, na hadu da cunkoson ababen hawa a kusa da Oke-Mosan, sakamakon ci gaba da aikin hanyar Abeokuta-Sagamu, da karkatar da tafiya da kuma rufe hanyar.
"Daga nan sai na sauka sannan kuma na hade da masu kula da zirga-zirga wajen saukake zirga-zirgar ababen hawa da ke kan tafiye-tafiyen su."
Dubi sakon a ƙasa:
Martani mabanbanta daga 'yan Najeriya
A lokacin rubuta wannan rahoton, sakon ya samu alamar likes kusan 2,000 tare da daruruwan tsokaci daga 'yan Najeriya.
Legit.ng ta tattaro wasu martani a kasa:
Adekoya Lanre ya ce:
"Kana iya yin hakan cikin sauki ya mai girma gwamna, ka zo yankin Sango kafin karkashin gada zuwa oju ore, ya tabarbare, hanyar ya rushe gaba ɗaya."
Kofoshi Bab's ya ce:
"Wannan shine dalilin da yasa aka zabe ka kuma shine dalilin da ya sa jihar Ogun baki daya ta baka damar ci, da morewa a kan asusun harajinsu. Don haka ba ka bukatar yabawa kanka ya Maigirma Gwamna saboda kayi aikinka."
Folasheycrown Oduola ya ce:
"Duk yaudara ne, zabe na zuwa kuma kun fara aiwatar da komai mai kyau, ina so in tambaya, Shin yankin Agbado crossing, Agbado oja, oke.aro, lambe, ijoko ba a jihar Ogun suke bane ???"
Aminat Irawo ta ce:
"Ya yi kyau kwarai da gaske, kana ɗaya daga cikin gwamnoninmu na ƙwarai, da fatan za ka ci gaba fiye da haka a zango na biyu."
A wani labari na daban, gine-gine biyu sun rushe a ranar Laraba a wurare daban-daban a cikin Jihar Anambra.
Yayin da wani bene mai hawa biyu da ake kan ginawa ya ruguje a kananan hukumomin Amikwo da Awka ta Kudu, sannan wani gini mai hawa biyu ya ruguje a Oko, a Karamar Hukumar Orumba.
Zuwa lokacin hada rahoton nan an ce an ceto mutum hudu daga cikin 20 da aka ce sun makale a karkashin baraguzan gine-ginen guda biyu.
Asali: Legit.ng