Mutum 20 sun makale karkashin baraguzan gine-gine guda biyu da suka rushe a Anambra

Mutum 20 sun makale karkashin baraguzan gine-gine guda biyu da suka rushe a Anambra

  • Wasu gine-ginen benaye guda biyu sun rufta a kananan hukumomi biyu a Jihar Anambra
  • Jami’ai sun ce an ceto mutum hudu cikin 20 da suka makale a karkashin baraguzan ginin
  • An dora alhakin ruftawar daya daga cikin ginin da ‘yin algus a cikin aiki

Gine-gine biyu sun rushe a ranar Laraba a wurare daban-daban a cikin Jihar Anambra.

Yayin da wani bene mai hawa biyu da ake kan ginawa ya ruguje a kananan hukumomin Amikwo da Awka ta Kudu, sannan wani gini mai hawa biyu ya ruguje a Oko, a Karamar Hukumar Orumba.

Zuwa lokacin da Punch ta hada rahoton nan an ce an ceto mutum hudu daga cikin 20 da aka ce sun makale a karkashin baraguzan gine-ginen guda biyu.

Wani ganau ya ce:

"Ginin da ya ruguje a Awka rufta ne da misalin karfe biyu na dare, inda ya fado kan wani bangare na wani bene mai hawa biyu, inda mutane da dama suka makale a ciki."

Jami'an gwamnati sun mamaye wajen

Jami’an hukumar raya yankin babban birnin Awka sun killace ginin.

Manajan Daraktan hukumar birnin, Ven. Amaechi Okwuosa ya ce an fara ginin ne tun shekara 10 da suka gabata kuma a shekarar 2018 an yi masa alama ta a rusa shi.

DUBA NAN: Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota

Mutum 20 sun makale cikin gine-gine guda biyu da suka rushe a Anambra
Mutum 20 sun makale karkashin baraguzan gine-gine guda biyu da suka rushe a Anambra
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Abin mamaki yayin da wani mutum ya kara aure da kudin tallafin da kungiya ta ba shi domin kula da ’ya’yansa 7

Ya ce,

“Duk da cewa maginin ya fara rushe ginin, ba a yi amfani da kayan aikin da ya dace ba, don haka ya ruguje. An ceto mutum hudu da suka ji raunuka daban-daban.”
Da yake magana a kan abin da ya faru a Oko, Shugaban Hukumar Kula da Tsara Birane ta Anambra, Chike Maduekwe, ya dora alhakin lamarin a kan "hada baki wajen yin algus a aiki."

Ya ce an rufe ginin, yayin da aka kira mai ginin zuwa ofishin hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel