Da duminsa: Kotu ta wanke tsohuwar ministan Buhari kan badakalar kwalin NYSC

Da duminsa: Kotu ta wanke tsohuwar ministan Buhari kan badakalar kwalin NYSC

  • Bayan watanni da ta dinga fuskantar zargi a kan kin yin hidimar kasa, kotu ta wanke Kemi Adeosun a Abuja
  • Wata babbar kotun tarayya a ranar Laraba, 7 ga watan Juli, ta ce tsohuwar ministan kudin na da dalilai gamsassu da suka sa bata yi NYSC ba
  • Mai shari'a Taiwa Taiwo ya yi bayanin cewa Adesoun bata yi hidimar kasa ba saboda shekarunta sun wuce lokacin da ta dawo Najeriya

Tsohuwar ministan kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli ta wanku a gaban kotu kan zarginta da ake da kin yi hidimar kasa ta NYSC.

Kamar yadda alkali mai shari'a, Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya dake Abuja ya yanke, bai dace ta yi hidimar kasan ba koda ta kammala digiri a shekaru 22 saboda har a lokacin 'yar Birtaniya ce, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Sunaye da tarihin likitoci 8 kacal da kasar Najeriya ke da su a karni na 19

KU KARANTA: Da duminsa: An garkame makarantun firamare a Abuja kan yajin aikin malamai

Kotun ta kara da cewa tsohuwar ministan ta dawo kasarta ta gado lokacin da ta wuce shekaru 30 a duniya, lamarin da yasa ba za ta iya hidimar kasa ba.

Har ila yau, Mai shari'a Taiwo ya ce wacce ake karar bata bukatar shaidar kammala NYSC kafin a nadata a matsayin minista a Najeriya, Leadership ta kara da cewa.

Wani sashi na hukuncin ya ce:

"Karin bayani game da wacce ake karan ya nuna cewa ta kasance 'yar Ingila tun a 1989 da ta kammala jami'ar gabas ta London dake Ingila lokacin da take da shekaru 22 a duniya kuma bata cancanci yin hidimar kasa ba kamar yadda dokar NYSC CAP N8, LFN, 2004 ta tanada."

A wani labari na daban, kungiyar malamai ta kasa baki daya (NUT), reshen jihar Kaduna, ta maka Gwamna Nasir El Rufai gaban kotun masana'antu kan zarginsa da take da kutse cikin al'amuranta.

A tare da gwamnan, kungiyar ta hada da antoni janar na jihar, hukumar makarantun firamare da kuma antoni janar na tarayyar Najeriya, Daily Nigerian ta ruwaito.

A lokacin da aka kira shari'ar gaban mai shari'a Ayodele Obaseki-Osaghae, lauyan mai kara, Samuel Atung ya sanar da kotun cewa an mikawa dukkan wadanda ake kara sammaci.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel