Lamari ya yi zafi: Sarkin Yarbawa ya shawarci Sunday Igboho ya mika kansa ga DSS

Lamari ya yi zafi: Sarkin Yarbawa ya shawarci Sunday Igboho ya mika kansa ga DSS

  • Wani sarkin gargajiya ya shawarci Sunday Igboho fa ya mika kansa ga hukumar DSS ta Najeriya
  • Sarkin ya bayyana haka ne biyo bayan sanar da farautar Sunday Igboho da DSS ke yi a yanzu
  • Ya ce bai kamata Sunday Igboho da tawagarsa su aikata irin wannan dangen aiki na kokarin ballewa ba

Jihar Osun - Sarkin gargajiya, Olowu Kuta kuma Shugaban Majalisar koli ta Owu Obas, Oba Hameed Makama, ya shawarci mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Ighoho, da ya mika kansa ga Ma’aikatar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa dake Owu Kuta a karamar hukumar Aiyedire a jihar Osun yayin hira da manema labarai.

Ya shawarci masu fafutukar ballewar da su tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, The Nation ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Wasu daga cikin daliban Baptist sama da 100 da aka sace sun kubuta

Lamari ya yi zafi: An shawarci Sunday Igboho da ya gaggauta mika kansa ga DSS
Mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Igboho | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya jaddada a taron majalisar sarakunan gargajiyan yankin cewa, babu wanda ya taba tattauna batun ballewa kuma sarakuna sun yi imani da hadin kan kasar nan.

Oba Makama ya ce:

“Babu wata gwamnatin da za ta so ta ga kasarta cikin rikici. Yakin neman ballewa daidai yake da amfani da makamai don yakar kasa.
“Babu wanda ya isa ya kalubalanci gwamnati kuma ya yi nasara. Najeriya ba za ta zauna ba, bayan yakin basasa, kuma ta sake fuskantar wani yakin cikin gida.
“Yan bindiga da 'yan Boko Haram da muke dasu yanzu sun isa. Don haka, zan ba masu fafutukar ballewa shawarar tattaunawa da Gwamnatin Tarayya
“Sunday Igboho ya kamata ya mika kansa ga gwamnati bisa son ransa. Za a ji tausayinsa maimakon su kamashi.”

Ya kara da cewa:

“Maimakon kira ga ballewa, zan goyi bayan sake fasalin kasa saboda idan aka sake tsari, to za a iya mika mulki. Idan aka karkata akalar mulki, za a samu karin kudi.

Sunday Igboho Ya Tura Sako Ga FG, Yana Neman Diyyar Makudan Kudade

Sunday Igboho a ranar Asabar ya rubuta takardar koke ga gwamnatin tarayya kan barnar da aka yi wa gidansa, motoci da sauran kadarori da jami'an tsaro suka yi, The Nation ta ruwaito.

Ya yi kiyasin asarar da ya yi cewa ya kai Naira miliyan 500 kuma ya nemi a biyashi wannan kiyasi.

Igboho, a cikin wata wasika ta hannun mai ba shi shawara Cif Yomi Alliyu (SAN) ya kuma nemi gafara daga jama'a kan abin da ya kira take hakkinsa da aka yi a lokacin da aka mamaye gidansa da kuma wani binciken da jami'an tsaro suka yi.

An Kame 'Yan Gangamin Kafa Kasar Yarbawa 47 Dauke da Layu, Zasu Bayyana a Kotu Gobe

A wani labarin, A wani labarin daban, Jihar Legas - A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo, rundunar 'yan sanda ta jihar ta cafke wasu daga cikin masu gangamin kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa a yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a jiya Asabar a cikin jihar.

Bayan tabbatar da kamun, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Hakeem Odumosu ya gabatar da wasu mutane 47 da aka kama a wurin zanga-zangar ta nuna goyon baya ga kafa haramtacciyar kasar Yarbawa.

An gabatar da hotuna, mazuban abinci, layu, da sauransu a matsayin abubuwan da aka kame yayin zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.