Bayan Najeriya, An Shigar da Karar Twitter a India Kan Yunkurin Cutar da Kasar

Bayan Najeriya, An Shigar da Karar Twitter a India Kan Yunkurin Cutar da Kasar

  • Rahoto ya bayyana cewa, wata kungiya a kasar Indiya ta maka kamfanin Twitter a kotu bisa zargin kutse cikin lamarinta
  • Kungiyar ta yi zargin cewa, Twitter na amfani da karfinta na Intanet wajen cutar da tsarin 'yan kasar dake amfani da ita
  • A baya Najeriya ta dakatar da Twitter bisa zargin yi mata katsa-landan cikin harkokin mulkinta ta hanyar goge rubutun shugaban kasa

Wata kungiya a India ta shigar da karar shugaban ofishin Twitter da ke kasar bayan da Twitter ya wallafa taswirar kasar a shafinta.

Taswirar ta nuna duka yankunan Jammu da Kashmir, wadanda ke rikici da Pakistan da kuma Ladak da ke yankin Buda a wajen Indiya.

Wannan dai ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta, amma daga baya an cire bangaren daga shafin Twitter.

KU KARANTA: Tsadar Abinci: CBN Ta Gano Mafita Kan Tsadar Masara, Za Ta Tallafawa 'Yan Kasa

Bayan Najeriya, An Shigar da Karar Twitter a India Kan Yunkurin Cutar da Kasar
Tambarin Twitter da Mutane rike da wayar salula | Hoto: outlookindia.com
Asali: UGC

Korafin da Praveen Bhatti shugaban kungiyar Baijrang Dal wata kungiyar sojoji a yankin Uttar Pradesh ya shigar, ya zargi shugaban ofishin da wasu mukarrabansa kan kokarin amfani da damar da suke da ita ta kafar intanet su wallafa abin da zai iya cutar da mutane.

Alakar dai da ke tsakanin Twitter da gwamnatin India ta samu matsala ne tun lokacin da ake zargin Twitter da kin bin sabbin dokokin da aka shimfida a kasar.

NCC Ta Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Hana ’Yan Najeriya Damar Hawa Twitter

A Najeriya kuwa, jaridar The Nation ta ruwaito cewa, kamfanonin sadarwa a Najeriya sun ce sun samu umarni daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) don aiwatar da dakatar da ayyukan karamin shafin yanar gizo na Twitter.

Kamfanonin da ke aiki a karkashin kungiyar masu lasisi na kamfanonin sadarwar na Najeriya (ALTON), sun ce sun gudanar da aikin tantance bukatar bisa ga kyakkyawan tsarin duniya.

Shugabanta, Gbenga Adebayo, a cikin wata sanarwa, ya ce:

“Mu, kungiyar masu lasisi na kamfanonin sadarwar na Najeriya (ALTON), muna son tabbatarwa cewa mambobinmu sun karbi umarni daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), mai kula da masana'antun da su dakatar samun damar isa ga Twitter."

KARANTA WANNAN: Tsadar Abinci: CBN Ta Kawo Mafita, Za Ta Karya Farashin Shinkafa a Najeriya

Dakatar Da Twitter: Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter

A wani labarin, Tsohon sanata daga yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana wata hanya mafi sauki ga mutanen da ke son hawa shafin Twitter duk da hanin da aka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan kafar sada zumunta ta Twitter bisa goge wani rubutu da shugaban kasar ya yi, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Shawarar da Shehu Sani ya bayar, ta tsaya ne kan 'yan Najeriya dake rayuwa a jihar Legas, da kuma duk wadanda ke rayuWa a jihohin dake kusa da iyakokin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.