2023: Zulum ya goyi bayan gwamnonin kudu kan mika mulki yankinsu

2023: Zulum ya goyi bayan gwamnonin kudu kan mika mulki yankinsu

  • Gwamna Zulum na Borno ya nuna goyon bayansa ga gwamnonin kudu kan cewa shugabancin kasa ya koma yankinsu
  • Ya sanar da yadda aka yi yarjejeniya a APC kan cewa arewa ta karba mulki, a 2023 a mika mulkin ga kudanci
  • Sai dai gwamnan ya ce siyasa ce kuma bai dace mutane su dinga cewa dole a bada mulki zuwa yankin kudu ba

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sake yin kira da a mika mulki yankin kudancin kasar nan inda ya goyi bayan zauren gwamnonin kudanci a matsayarsu ta zaben yankin da zai yi shugabancin kasa a 2023.

A wani taro da gwamnonin kudancin suka yi a Legas a ranar Litinin, sun aminta da cewa yankinsa ne ya dace ya fitar da shugaban kasa na gaba idan za a duba adalci da daidaito, lamarin da Zulum ya bada goyon baya.

KU KARANTA: NUT ta maka Gwamna El-Rufai'i da wasu mutum 3 a gaban kotu

2023: Zulum ya goyi bayan gwamnonin kudu kan mika mulki yankinsu
2023: Zulum ya goyi bayan gwamnonin kudu kan mika mulki yankinsu. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Sunaye da tarihin likitoci 8 kacal da kasar Najeriya ke da su a karni na 19

"Na fadi ba sau daya ba ko biyu, Ni Farfesa Babagana Zulum, na tsaya a matsayar cewa a mika shugabancin kasa zuwa yankin kudu a 2023 saboda hadin kan kasar nan yana da amfani," gwamnan ya sanar a wata tattaunawa da aka yi da shi a Channels TV a shirin gari ya waye na ranar Laraba.

Akwai yarjejeniyar mika mulki ga kudu a 2023 a APC

"Abu na biyu, hadaka tana da matukar amfani. Na uku, ni a APC nake, shekaru shida zuwa bakwai, APC ta bada tikitin shugabancin kasa ga arewacin Najeriya da yarjejeniyar cewa a 2023 za a bai wa kudu."

Gwamnan ya sakankace cewa shugabannin kudu suna da iko da hakkin bukatar a basu shugabancin kasa amma ya ce ba kuma zai zama dole hakan ba.

Siyasa ce, a cire kalmar dole

"Amma kuma wannan siyasa ce. Ya kamata mu zauna mu tattauna kan lamarin siyasa a tsakaninmu," yayi bayani yayin da yake jan kunne kan rura rigimar siyasa kafin 2023.

“Kalmar da jama'a ke cewa dole ne a mika shugabancin kasa yankin kudu, ina so jama'a su cire kalmar dole a ciki."

A wani labari na daban, Malaman makarantun firamare na gwamnati a karamar hukumar Bwari dake Abuja sun fara yajin aiki kan tsaikon da aka samu na biyansu albashin watan Yuni.

An fara yajin aikin ana sauran kwanaki biyu jarabawar zangon karatu na uku na wannan shekarar a babban birnin tarayyan, Daily Trust ta ruwaito.

Wata malamar makaranta dake Kubwa da ta bukaci a boye sunanta ta sanar da Daily Trust cewa kungiyar malamai ta kasa reshen karamar hukumarsu ta bada takarda inda take sanar da cewa za ta fara yajin aikin a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: