Da duminsa: Hotunan Buhari yana kawata sabon COAS, yana jagorantar FEC a Aso Villa

Da duminsa: Hotunan Buhari yana kawata sabon COAS, yana jagorantar FEC a Aso Villa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawata COAS Manjo Janar Farouk Yahaya a gidan gwamnati
  • Hakan ya biyo bayan tantance sabon shugaban rundunar sojin kasan da majalisar tarayya tayi
  • Har ila yau, shugaba Buharin yana jagorantar taron majalisar zartarwa ta kasa a gidan gwamnati dake Abuja

Aso Villa, Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawata sabon shugaban rundunar hafsin soja, Manjo Janar Farouk Yahaya a gidan gwamnati dake Abuja.

Hakan ya biyo bayan tabbatar da shi da majalisar tarayyar kasar nan tayi a matsayin sabon shugaban rundunar bayan tantancesa da tayi a gaban majalisar.

KU KARANTA: Da duminsa: Ana musayar ruwan wuta tsakanin 'yan daba da jami'an tsaro a Legas

Da duminsa: Hotunan Buhari yana kawata sabon COAS, yana jagorantar FEC a Aso Villa
Da duminsa: Hotunan Buhari yana kawata sabon COAS, yana jagorantar FEC a Aso Villa. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ku gaggauta ceto dukkan dalibai da aka sace, Buhari ga hukumomin tsaro

Hadimin shugaban kasan, Femi Adesina ne ya wallafa hotunan da safiyar ranar Laraba, 7 ga watan Yulin 2021 a shafinsa na Facebook.

Buhari yana jagorantar FEC

Kamar yadda Adesina ya sanar, shugaban kasan bayan kawata sabon COAS din, yana shugabantar taron majalisar zartarwa ta kasa a gidan gwamnatin tarayyan.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel