Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Dilip Kumar ya riga mu gidan gaskiya

Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Dilip Kumar ya riga mu gidan gaskiya

  • Allah ya yi wa tsohon jarumin fina-finan Indiya, Dilip Kumar rasuwa
  • Fitaccen jarumin ya bar gidan duniya yayin da yake da shekaru 98 a duniya
  • Tauraron fina-finan ya yi suna kuma ya rasu a ranar Laraba inda kasar ta kacame da ta'aziyyarsa

Dilip Kumar, daya daga cikin fitattun taurarin fina-finan Indiya, ya rasu a ranar Laraba yana da shekaru 98, lamarin da ya kawo ta'aziyya daban-daban a fadin kasar Indiya, The Guardian ta ruwaito

Tare da Dev Anand da Raj Kapoor, Kumar yana daya daga cikin sunaye uku da suka yi tashe a silmar Indiya daga 1940 zuwa 1960 inda ya kwashe sama da shekaru 50 yana tashe kuma yayi fina-finai sama da 60.

KU KARANTA: Rai 1 ta sheka lahira yayin da 'yan sanda suka kai samame maboyar masu satar jama'a

Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Dilip Kumar ya riga mu gidan gaskiya
Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Dilip Kumar ya riga mu gidan gaskiya. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku gaggauta ceto dukkan dalibai da aka sace, Buhari ga hukumomin tsaro

Jarumin da aka fi sani da "The Tragedy King" kyakyawa ne mai gashi kayatacce tare da babbar murya, ya jagoranci wasu masana'antun fina-finai na India na kudi kuma an samu tarin nasarori.

Jarumin bai zama gwarzon duniya ba

Sai dai kuma jarumin bai samu damar gwarzantaka a duniya ba ya ki fitowa a Sherif Ali na Dabid Leans 1962 a film mai suna "Lawrence of Arabia". An dauka bangaren an baiwa Omar Sharif dan asalin kasar Egypt.

Tsatson shi da lokacin haihuwarsa

Muhammad Yusuf Khan ne mahaifin Kumar inda aka haife shi a ranar 11 ga watan Disamban 1922 a Peshawar, Pakistan, a lokacin kasar na wani sashi na inda Birtaniya ke mulka.

Mahaifinsa dan kasuwar kayan marmari wanda a wurin sana'ar ne suka hadu da jaruma Devika Rani har ta kai shi ga yin fim , Channels TV ta ruwaito.

A wani labari na daban, 'yan daba wadanda aka fi sani da Area Boys a jihar Legas suna musayar wuta da jami'an tsaron hadin guiwa a Apapa dake jihar Legas a halin yanzu.

Jami'an tsaron hadin guiwar sun hada da 'yan sanda, jami'an hukumar kula da cunkoson tituna na jihar Legas da sojoji.

Ganau sun ce jami'an tsaron hadin guiwar sun isa get na farko na Tin-Can dake Mile 2 babbar hanyar Apapa domin fatattakar bata-garin da ake zargi da aikata laifuka a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng