Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Jigon PDP

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Jigon PDP

  • Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwa ye ba sun yi awon gaba da jigon PDP a jihar Edo, Ugbo Iyiriaro
  • Rahoto ya nuna cewa yan bindigan sun farmaki jigon PDP ne yayin da yake kan hanyarsa zuwa mahaifarsa
  • Hukumar yan sandan jihar Edo, ta tabbatar da faruwar lamarin, amma tace bata samu cikakken bayani ba daga DPO

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da jigon jam'iyyar PDP a jihar Edo, Ugbo Iyiriaro, a kan hanyar Benin-Abraka, kuma sun nemi a biya miliyan N20m, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Jam'iyyar APC Zata Ladaftar da Ministan Buhari Saboda Cece-Kuce da Gwamna

Wani rahoto daga majiyar jami'an tsaro a Benin, babban birnin Edo, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a tsakanin Ugo da Ugboko, karamar hukumar Orhionmwon ranar Talata, kamar yadda tribune ta ruwaito.

Yan bindiga sun sace jigon PDP a Edo
Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Jigon PDP Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Iyiriaro, ya bar Benin domim halartar wani lamari na gaggawa da ya taso a mahaifarsa Umoghunokhua dake ƙaramar hukumar Orhionmwon, kafin yan bindigan su sace shi yana tsaka da tafiyarsa.

Hukumar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin.

Da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Edo, Bello Kontongs, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Amma ya bayyana cewa har yanzun hukumar yan sanda ba ta samu rahoto a hukumance daga DPO dake yankin ba.

KARANTA ANAN:Da Ɗuminsa: Sanatoci Sun Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Na Sake Karɓo Bashin Tiriliyan N2.3tr

"Eh, mun samu labarin abinda ya faru, amma har yanzun DPO dake yankin bai kawo mana cikakken abinda ya faru a hukumance ba." inji shi.

A wani labarin kuma Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

Gwamnan Borno , Babagana Zulum, yace hana makiyaya kiwo a fili a wasu jihohin ƙasar nan ba zai yi aiki ba har sai an magance matsalar tsaro.

Gwamnan yace abinda ya kamata a maida hankali akai shine lalubo hanyar magance matsalar tsaro da ta abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel