Sunaye da tarihin likitoci 8 kacal da kasar Najeriya ke da su a karni na 19

Sunaye da tarihin likitoci 8 kacal da kasar Najeriya ke da su a karni na 19

'Yan Najeriya masu tarin yawa na cigaba da karanta fannin lafiya domin tseratar da rayuka da kuma zaunar da duniyar lafiya.

Jama'a da yawa basu san mutum takwas na farko a kasar nan da suka fara zama likitoci ba a karni na 19 a Najeriya.

Legit.ng tana gabatar muku da mutum takwas na farko a Najeriya da suka fara zama likitoci a karni na 19, wanda ta samo daga My Engineers.

KU KARANTA: Cikakken sunayen janarori 114 da sauran sojin kasa da aka sauyawa wurin aiki

Sunaye da tarihin likitoci 8 kacal da kasar Najeriya ke da su a karni na 19
Sunaye da tarihin likitoci 8 kacal da kasar Najeriya ke da su a karni na 19. Hoto daga My Engineers
Asali: UGC

KU KARANTA: Dama na sha alwashin kai ka kasa, Asari Dokubo yayi martani kan kamen Nnamdi Kanu

1.William Broughton Davies (1833-1906)

William Broughton Davies an haife shi a Sierra Leone kuma dan tsoffin bayi ne. Davies ya yi karatu a Ingila inda ya zama likita.

Bayan nan ya tafi Scotland inda ya samu MD a 1858 bayan jarabawar da yayi a jami'ar Edinburgh a 1859.

2 James Africanus Beale Horton (1835-1883)

Kamar Davies, Horton da ne ga tsoffin bayi amma na kabilar Ibo. Ya samu karatun shi a Ingila.

Ya koma Scotland bayan ya samu horarwa kuma ya samu MD a 1859 daga jami'ar Edinburgh.

3. Nathaniel King (1847-1884)

Yarabawan iyaye ne suka haifa Nathaniel King a kasar Sierra Leone. Shine dan Najeriya na farko da ya fara aiki da ilimin likitancin zamani a kasarsa.

King yana daya daga cikin dalibai hudu na farko da aka fara yi wa horon karatun likitanci a Najeriya. Ya cigaba da karatun shi na likitanci a Ingila.

4. Obadiah Johnson (1849-1920)

An haifa Obadiah Johnson a Sierra Leone. Ya samu digirinsa na farko a kwalejin Fourah Bay a 1879 kuma ya karasa kwalejin King's inda ya samu M.R.S.C da L.S.A a 1884.

Ya samu M.D a jami'ar Edinburg bayan ya mika rubutun da yayi kan magungunan Afrika ta yamma a 1889.

5. John Randle (1855-1928)

An haifa Randle a kasar Sierra Leone kuma mahaifinsa 'yantaccen bawan Yarabawa ne. Ya kammala karatunsa a jami'ar Edinburgh a 1888 da M.B da C.M.

6. George Stone Smith (1863-1940)

George Stone Smith wanda daga bisani ya sauya sunan shi zuwa Orisadipe Obasa an haife shi a Sierra Leone.

Mahaifinsa da ne ga Elekole na Ikole-Ekiti kuma mahaifiyarsa 'yar gidan sarauta ta Akija dake Ikija a Abeokuta.

7. Sodeinde Akinsiku Leigh-Sodipe (1865-1901)

Sodeinde Akinsiku Leigh-Sodipe shine dan Najeriya na farko dake da sunan Najeriya. An haife shi a Legas kuma ya halarci kwalejin horar da likitoci dake Newcastle. Ya samu digirinsa na M.B a jami'ar Durham a 1892

8. Alexander Williams (1861-1935)

Alexander Williams wanda aka fi sani da Oguntola Odunbaka Sapara an haife shi a Sierra Leone. Mahaifinsa 'yantaccen bawa ne daga Ilesha a jihar Osun kuma mahaifiyarsa daga Egbaland take.

A wani labari na daban, hukumar kula da al'amuran 'yan sanda ta shirya tsaf domin yi wa Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa zagon kasa (EFCC), karin girma zuwa mataimakin sifeta janar na 'yan sanda a wannan makon, TheCable ta fahimci hakan.

Magu, wanda aka karawa girma zuwa kwamishinan 'yan sanda a 2018, an bukaci cireshi daga matsayin shugaban EFCC bayan kammala binciken kwamitin Jastis Ayo Salami bayan an zargesa da yin amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Kwamitin ya bukaci a tsige Magu daga kujerarsa saboda kasa bayyana inda kudade har N431,000,000 na kudin yada labarai da aka sakarwa ofishin shugaban hukumar EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 zuwa Mayun 2020 suke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel