NUT ta maka Gwamna El-Rufai'i da wasu mutum 3 a gaban kotu

NUT ta maka Gwamna El-Rufai'i da wasu mutum 3 a gaban kotu

  • Kungiyar Malamai ta Kasa reshen jihar Kaduna ta kai karar Gwamna Nasir ElRufai gaban kotun masana'antu
  • Kungiyar ta hada da antoni janar na jihar Kaduna, hukumar makarantun firamare ta jihar da antoni janar Malami
  • Ta zargesu da katsalandan tare da kutse a al'amuranta wanda tace ba zata lamunci hakan ba

Kaduna

Kungiyar malamai ta kasa baki daya (NUT), reshen jihar Kaduna, ta maka Gwamna Nasir El Rufai gaban kotun masana'antu kan zarginsa da take da kutse cikin al'amuranta.

A tare da gwamnan, kungiyar ta hada da antoni janar na jihar, hukumar makarantun firamare da kuma antoni janar na tarayyar Najeriya, Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: Dalla-dalla: Za a yi wa Magu karin girma zuwa AIG duk da zargin rashawa

NUT ta maka Gwamna El-Rufai'i da wasu mutum 3 a gaban kotu
NUT ta maka Gwamna El-Rufai'i da wasu mutum 3 a gaban kotu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Lauya daya ya bayyana a kotu

A lokacin da aka kira shari'ar gaban mai shari'a Ayodele Obaseki-Osaghae, lauyan mai kara, Samuel Atung ya sanar da kotun cewa an mikawa dukkan wadanda ake kara sammaci.

Wadanda aka yi kara na farko, na biyu da na uku basu turo wakilansu ba ballantana lauyoyinsu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Lauyan wanda ake kara na hudu, O.A Akinde ta tabbatar da cewa an kawo musu sammaci kuma sun yi martani ga kotun.

Ta kara da yin bayanin cewa an sanar da ita cewa sai martaninsu ya kwashe kwanakin da ya dace kafin a duba martanin.

Akinde ta bukaci kotun da ta dage sauraron shari'ar da fatan kotun za ta kaiwa sauran wadanda ake kara sammaci.

KU KARANTA: COAS Yahaya ya gwangwaje tsohon jarumin fim Samanja da kyautar N2m

A wani labari na daban, hukumar kula da al'amuran 'yan sanda ta shirya tsaf domin yi wa Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa zagon kasa (EFCC), karin girma zuwa mataimakin sifeta janar na 'yan sanda a wannan makon, TheCable ta fahimci hakan.

Magu, wanda aka karawa girma zuwa kwamishinan 'yan sanda a 2018, an bukaci cireshi daga matsayin shugaban EFCC bayan kammala binciken kwamitin Jastis Ayo Salami bayan an zargesa da yin amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Kwamitin ya bukaci a tsige Magu daga kujerarsa saboda kasa bayyana inda kudade har N431,000,000 na kudin yada labarai da aka sakarwa ofishin shugaban hukumar EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 zuwa Mayun 2020 suke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng