Annobar Korona: An Garkame Wasu Makarantu Biyu Saboda Tsoron Ta'azzarar Korona

Annobar Korona: An Garkame Wasu Makarantu Biyu Saboda Tsoron Ta'azzarar Korona

  • Wasu makarantu masu zaman kansu sun kai rahoton bukatar rufe makarantun bisa tsoron Korona a jihar Legas
  • An ruwaito cewa, makarantun sun kai rahoto ne ga ma'aikatar ilimi, wacce ta zo ta gudanar bincike a kai
  • Hakazalika, a wani banagare guda, jihar Kaduna ta kulle makarantunta kuwa saboda tsoron harin 'yan bindiga

An rufe wasu makarantu biyu masu zaman kansu a yankin Lekki da ke jihar Legas saboda tsoron barkewar annobar Korona.

Makarantun da aka garkame su ne Lagoon Girls’ Secondary School da Standard Bearer School.

Legit.ng Hausa ta ruwaito daga jaridar The Nation cewa, ta samu labari daga wata majiya a Ofishin tabbatar da ingancin Ilimi, a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Legas cewa an rufe makarantun ne bayan da suka kawo rahoton kansu ga ma’aikatar wanda ya kai ga jami’ai suka ziyarce su.

KARANTA WANNAN: Karin Bayani: Gwamnonin Kudu sun ce basu amince a sake kame wani a yankinsu ba sai da izininsu

Annobar Korona: An Garkame Wasu Makarantu Biyu Saboda Tsoron Ta'azzarar Korona
Annobar Korona | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce:

“Daga abin da na tattara, bana tsammanin ofishinmu ne ya gano makarantun. Makarantun ne suka ba da rahoton kansu. Ba iya samun magana da shugabannin tawagar da suka je wurin ba domin su ba ni cikakken bayanin abinda ya faru lokacin da suka isa wurin."

El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna

Sabanin matsalar annobar Korona, gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin rufe wasu makarantu 13 nan take a wurare daban-daban a jihar, The Cable ta ruwaito.

Shugaban sashin kula da ingancin kayayyaki na ma'aikatar ilimi na jihar Kaduna, Umma Ahmed ce ta fitar da sanarwa.

An aike da sanarwar da shugabannin makarantu masu zaman kansu da abin ya shafa, sakon na mai cewa nan take za su rufe makarantun.

Ta kuma yi gargadin hukuncin da ka iya biyo baya idan ba a bi umurnin ba.

KARANTA WANNAN: Lamari ya yi zafi: Sarkin Yarbawa ya shawarci Sunday Igboho ya mika kansa ga DSS

Jihar Legas za ta sanya dokar hana gabatar da wadanda aka kame da laifi a gaban 'yan jarida

A wani labarin daban, Majalisar dokokin jihar Legas ta zartar da kudirin gyaran dokar Kundin Laifuka ta 2015 a jihar, wacce ke neman hana ‘yan sanda gabatar da wadanda ake zargi a gaban 'yan jarida, The Cable ta ruwaito.

Kudirin gyaran, mai taken: ‘Bill of Administration of Criminal Justice (Amendment) Bill, 2021’, an mika shi ne a ranar Litinin a yayin zaman da mataimakin kakakin majalisar, Wasiu Eshilokun-Sanni ya jagoranta.

A dokar gyaran, sashi na 9 (a) ya ce:

"Tun daga lokacin wannan dokar zata fara aiki, 'yan sanda za su daina gabatar da duk wani wanda ake zargi a gaban manema labarai".

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.