Da Duminsa: Ministar Buhari da ta yanki jiki ta fadi ta farfado, an sallame ta daga asibiti
- An sallami ministar Buhari da ta yanki a i daga asibiti bayan kwana a asibiti a Bauchi
- Rahoto ya bayyana cewa, gajiya ne ya sanya ministar yankan jiki ta fadi a yayin da take jawabi
- Hakazalika an dauke ta zuwa babban birnin tarayya Abuja domin kula da ita na musamman
An sallami Karamar Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Ambasada Maryam Katagum, wacce ta yanki jiki ta fadi a yayin wani taron karawa juna sani a ranar Litinin a Jihar Bauchi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Katagum wacce ta je jihar Bauchi domin kaddamar da shirin karfafa gwiwa ta yanki jiki ta fadi yayin da take kokarin gabatar da jawabinta.
An garzaya da ita zuwa cibiyar kula da masu rauni a asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa.
KARANTA WANNAN: Saura Kiris a Cimma Kudurin Haramta Barace-Barace a Jihar Katsina
Ministar, wacce ta fito daga karamar hukumar Katagum da ke jihar Bauchi, ta kasance a jihar tun ranar Asabar kuma ta yi alkawura da dama da daukar ayyuka kafin ranar Litinin lokacin da ta yanki jiki fadi.
Majiyar da ta ziyarci cibiyar da lamarin ya faru a ranar Talata, ta ce daya daga cikin jami’an tsaron da ke bakin kofa a cibiyar ya fada cewa an dauke ministar daga cibiyar ta kula da masu rauni zuwa dakin kula na musamman a asibitin da ta kwanta.
An ruwaito cewa an sallami ministar
A sashen kula na musamman, wata ma’aikaciyar jinya ta ce an sallami ministan.
Wata ma’aikaciyar jinya wacce ta ki bayyana sunanta ta ce:
“Jiya an kawo ministar domin kula da lafiyar ta. Anan ta kwana kuma an sallameta.
“Ta sha wahala ne saboda gajiya kuma an sallame ta da misalin karfe 9 na safe saboda ta samu sauki. An mayar da ita Abuja.”
Yadda aka mayar da ministan Buhari da ta yanki jiki ta fadi zuwa dakin asibiti
Karamar ministar masana'antu, cinikayya da hannun jari, Ambasada Maryam Yalwaji Katagum, wacce ta yanke jiki ta fadi a wani taro a ranar Litinin ta fara samun lafiya kuma an mayar da ita dakin asibiti dake asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.
Kamar yadda wata majiya ta sanar da Daily Trust, shugaban asibitin, Dr Yusuf Jibrin Bara ya dauka ministan da kan shi inda ya kaita dakin kwantar da marasa lafiya na asibitin.
Karin bayani na nan tafe...
KARANTA WANNAN: Mafita: Matasan Katsina sun shirya horar da yadda za a fatattaki 'yan bindiga
Dukobo Asari ya caccaki Nnamdi Kanu
A wani labarin, A wani labari na daban, Mujahid Asari Dokubo, tsohon kwamandan tsageru kuma shugaban gwamnatin gargajiya ta Biafra, yayi martani bayan sake kama Nnamdi Kanu, shugaban IPOB da gwamnatin tarayya ta yi.
Kanu, wanda ke fuskantar tuhuma kan cin amanar kasa, ya tsallake beli bayan wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta sake shi saboda matsalar lafiya, Daily Trust ta ruwaito.
Ya tsere zuwa Ingila inda ya dinga bada umarni ga mambobin IPOB na kudu maso gabas a kan tada hazo a yankin. An sake kama shi a kasar waje kuma an dawo da shi Najeriya a ranakun karshen makon da ya gabata.
Asali: Legit.ng