Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun bindige mutum 18 a Adamawa

Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun bindige mutum 18 a Adamawa

  • Mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kai farmaki kauyen Dabna dake kusa da Garka a jihar Adamawa
  • Miyagun sun bindige rayuka 18 a kauyen dake karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa a safiyar Laraba
  • Ganau sun tabbatar da cewa rabin jama'ar garin sun tsere yayin da kauyukan kusa ke zaune cikin tashin hankali

Hong, Adamawa

Hankula a halin yanzu tashe suke a kauyen Garka dake karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa sakamakon farmakin da mayakan ta'addanci na Boko Haram suka kai kauyukan dake makwabtaka da su.

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Boss Mustapha, dan asalin garin Garka ne.

Jama'ar kauyukan kusa na cikin tashin hankali

A halin yanzu mazauna Garka na rayuwa a cikin tsoro bayan kashe a kalla mutum 18 da aka yi a kauyen Dabna da suke da makwabtaka.

KU KARANTA: Rai 1 ta sheka lahira yayin da 'yan sanda suka kai samame maboyar masu satar jama'a

Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun bindige mutum 18 a Adamawa
Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun bindige mutum 18 a Adamawa
Asali: Original

KU KARANTA: Sunaye da tarihin likitoci 8 kacal da kasar Najeriya ke da su a karni na 19

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru a sa'o'in farko na ranar Laraba. Daya daga cikin mazauna yankin ya ce rabin jama'ar garin sun koma kauyuka masu makwabtaka da su.

Mazauna kauyen sun tabbatar da cewa akwai yuwuwar maharan su fada kauyen Garka.

Wadanda suka sha da kyar sun bada labari

Wata wacce ta tsallake rijiya da baya mai suna Hilda Joshua, ta ce baya ga wadanda aka kashe, akwai wadanda suka samu miyagun raunika.

Ta kara da cewa da kyar ta sha inda ta tsere zuwa daji amma wasu daga cikin 'yan gidansu da makwabtansu suna kauyen, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mutum na daban ya ce baya ga wadanda aka kashe cikin kauyen, ya ga gawawwaki uku kwance a daji wurin Kwapre, wani kauye mai makwabtaka.

Jiragen yakin sojoji sun kai dauki

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an ga jiragen yakin sojoji na kaiwa da kawowa wurin kauyen inda suke wa maharan luguden wuta.

A wani labari na daban, hukumar kula da al'amuran 'yan sanda ta shirya tsaf domin yi wa Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa zagon kasa (EFCC), karin girma zuwa mataimakin sifeta janar na 'yan sanda a wannan makon, TheCable ta fahimci hakan.

Magu, wanda aka karawa girma zuwa kwamishinan 'yan sanda a 2018, an bukaci cireshi daga matsayin shugaban EFCC bayan kammala binciken kwamitin Jastis Ayo Salami bayan an zargesa da yin amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Kwamitin ya bukaci a tsige Magu daga kujerarsa saboda kasa bayyana inda kudade har N431,000,000 na kudin yada labarai da aka sakarwa ofishin shugaban hukumar EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 zuwa Mayun 2020 suke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng