Rai 1 ta sheka lahira yayin da 'yan sanda suka kai samame maboyar masu satar jama'a

Rai 1 ta sheka lahira yayin da 'yan sanda suka kai samame maboyar masu satar jama'a

  • Wani mai garkuwa da mutane ya wulla lahira bayan 'yan sanda sun kai samame maboyarsu a Imo
  • An gano cewa miyagun sun je har kofar gida sun sace wani mutum, lamarin da yasa 'yan sanda suka bibiyesu
  • An yi nasarar ceto mutum 1 sannan dan sanda ya samu rauni yayin da suaran miyagun suka tsere da raunika

Mai garkuwa da mutane daya ya sheka lahira kuma an ceto mutum daya da aka sace a wani samamen da 'yan sanda suka kai sansanin masu garkuwa da mutane a dajin Ehime Mbano dake Imo.

'Yan sanda sun samu rahoto a ranar 1 ga watan Yuli na sace wani Uzondu Kaka mai shekaru 46 dan salain Umunuma Okohia Isiala, Mbano, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Cikakken sunayen janarori 114 da sauran sojin kasa da aka sauyawa wurin aiki

Rai 1 ta sheka lahira yayin da 'yan sanda suka kai samame maboyar masu satar jama'a
Rai 1 ta sheka lahira yayin da 'yan sanda suka kai samame maboyar masu satar jama'a. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalla-dalla: Za a yi wa Magu karin girma zuwa AIG duk da zargin rashawa

'Yan bindigan sun yi amfani da wata mota kirar SUV inda suka sace shi a kofar gidansa, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan sanda sun bibiyi maboyar masu garkuwa da mutanen inda suka same su a dajikan Ehime Mbano.

"Bayan 'yan ta'addan sun hango jami'an tsaron, sai suka fara sakar musu ruwan wuta inda a nan wanda ake zargi daya ya mutu yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika kuma aka ceci wanda suka sace," Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abatam yace.

"Daya daga cikin jami'an ya samu rauni sakamakon harbin bindiga inda aka gaggauta mika shi asibiti.

"An samu harsasai, bindigogi da kuma salataf na rufe idon jama'a. Wanda aka sacen ya sanar da 'yan sandan cewa sun kwace masa N150,000, katin ATM din shi da sauransu.

“An mika gawar wanda ake zargin zuwa asibitin tarayya dake Owerri na jihar Imo. Ana kokarin ganin an cafke wadanda ake zargin da suka tsere da harbin bindiga."

A wani labari na daban, shugaban rundunar sojin kasa, COAS Manjo Janar Faruk Yahaya a ranar Litinin ya gwangwaje tsohon jarumin fina-finai, Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama da kyautar naira miliyan biyu a Kaduna.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa COAS ya bada wannan kyautar ne bayan ya ziyarci tsohon jarumin a gidansa.

NAN ta ruwaito yadda jarumin ya karyata rade-radin dake yawo na cewa ya mutu a kafafen sada zumunta a kwanakin da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel